Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Haɗin gwiwa na ‘yan sanda da jami’an tsaro na al’umma CWC sun sami nasar daƙile yunƙurin fashi da makami a ƙaramar hukumar Faskari ta Jihar Katsina.
Wata sanarwa ɗauke da sa hannun jami’in hulɗa da jama’a na ‘yan sanda a Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya ce wasu mutane da ake zargi ƴan fashi da makami ne suka afkawa Abu Iro ɗan shekara 23 inda sukai ƙoƙarin hallaka shi a garin Faskari.
Sai dai haɗin gwiwa na jami’an tsaron ƙarƙashin DPO na Faskari suka kawo wa matashin ɗaukin gaggawa.
DSP Abubakar Sadiq ya tabbatar da cewa jami’an tsaron sun sami nasarar ceto matashin,sai dai ɗaya daga cikin ɗan fashin ya sare shi a kai.
Haka kuma ɗaya daga cikin jami’an tsaro na al’umma CWC ya sami rauni a arangama da sukayi da ƴan fashin da yanzu suna asibitin Faskari ana masu magani inji Sadiq.
‘Yan sandan sun gano bindiga kiran AK 47 da babur guda ɗaya.
Kwamishinan ‘yan sanda a Jihar Katsina CP Bello Shehu ya yabawa jami’an tsaron ga yadda suka daƙile fashin cikin gaggawa.
Ya kuma tabbatar wa al’ummar jihar cewa jami’an sa ba za su gajiya ba wajen kare lafiya da dukiyar su ba.
