Muna murna da naɗin da Sarki Sanusi ya yi na Yariman Kano – Hajiyar Masallaci

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano 

Hajiya Hadiza Ali Bala ɗaya daga cikin ‘ya’yan Marigayi Galadiman Kano Abbas Sanusi da aka fi sani da Hajiyar Masallaci, kuma ake kiranta da “Sardaunar mata” ta bayyana naɗin da Sarkin Kano Muhammad Sanusi ya yi wa na Yariman Kano daga gidan su abin farin ciki ne gare su zuriyar Marigayi Galadiman Kano Abbas Sanusi.

Ta bayyana hakan ne a yayin wata walima da aka gudanar na taya murna ga wasu daga waɗanda aka yi wa sabbin naɗe-naɗen manyan sarautu a fadar Kano.

Ta ce ta yi mutuƙar jin daɗin yadda taga al’umma suka zo daga sassa daban-daban daga ciki da wajen jihar Kano suka taya su murnar wannan naɗin da Sarkin ya yi a masarautar Kano.

Ta ce wannan naɗe-naɗen muƙamai da aka yi duk sun shafe ta domin wanda aka bai wa Galadima a yanzu Baba Mannir uba ne a gare ta, haka wanda aka baiwa wambai ɗan’uwnata ne kuma ƙaninta  haka shima wanda aka baiwa Yariman  Kano  Ahmad Abbas Sanusi wanda suke  kiransa ɗan darman ƙanin ta ne kuma ɗanta.

Hajiya Hadiza Ali Bala “Sardaunan Mata ‘ta yi fatan dukkan waɗanda aka naɗa a muƙaman a masarautar Kano Allah ya ba su ikon riƙewa da sauke nauyin da aka ɗora musu

By ukarofi