
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnatin Jihar Kano ta amince da ware kimanin Naira biliyan 3 domin biyan kudin jarrabawa ga dalibai ƴan jihar guda 141,745.
Haka kuma ta fitar da sakamakon jarrabawar daliban da suke shirin kammala karatu a makarantun babbar sakandare na shekarar 2024.
Ta kuma jaddada aniyarta ta cigaba da samar da ilimi mai inganci acikin dalibai a jihar da kuma saukake masu halin biyan kudin karatu.
Kwamishinan Ilimi a jihar, Alhaji Haruna Makoda ya fadi hakan a yayin ganawa da manema labarai, ranar Asabar.
Ya ce, gwamnatin ta dauki matakin ne wanda bangare ne na aikin gyara harkar ilimi a jihar a karkashin Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Kwamishinan ya kuma ce, waɗanda za su amfana da tallafin sune daliban makaratun gwamnati da ke karkashin hukumomin KERD da STSB da kuma AIED.
Alhaji Haruna Makoda ya ce, za a biya wa daliban baki daya kudaden rubuta jarrabawa na NECO da NABTEB da NBAIS da kuma na SSCE a mataki na kasa.
Har’ilyau, kwamishinan ya bayyana cewa za a sanar da su karin bayanai game da tsarin ta hukumomin KERD da STSB da AIED.
