Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Akwai yiwuwar masu amfani da shafukan Facebook da na instagram a Nijeriya za su ga ɗib bayan da kamfanin da ya mallaki shafukan, wato Meta ya koka kan ɗimbin tara da gwamnati ta lafta masa wadda ya ce “ba abu ne mai yiwuwa ba”.
A bara ne hukumomin sanya ido uku na Nijeriya suka lafta wa kamfanin tarar da ta kai fiye da dala miliyan 290, bisa zargin kamfanin da karya wasu dokoki.
Sai ga shi kuma kamfanin na Meta ya yi rashin nasara a ƙarar da ya shigar a wata babbar kotu da ke Abuja, inda ya ƙalubalanci matakin.
“Za a iya tursasa wa mai shigar da ƙara ya rufe ayyukan shafin Facebook da instagram a Nijeriya domin rage hatsarin da zai iya faɗawa ciki idan bai bi umarnin ba,” kamar yadda kamfanin ya rubuta a takardun shigar da ƙara.
Meta ne kuma kamfanin da ya mallaki manhajar WhatsApp, to amma kamfanin bai ambaci WhatsApp ɗin ba a bayanin nasa.
Babbar kotun ta bai wa kamfanin wa’din zuwa ƙarshen watan Yuni ya biya tarar.
An tuntuɓi kamfanin Meta kan matakin da zai ɗauka amma bai bayar da amsa ba.
Facebook ne shafin da al’umma suka fi amfani da shi a Nijeriya, inda miliyoyin al’ummar ƙasar ke amfani da shi a kowace rana.
