Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatin Nijeriya ta ce, barazanar da kamfanin Meta ya yi na ficewa daga ƙasar, ba zai hana a hukunta shi ba.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da darektan Hukumar Sa Ido kan Farashi da Kare Haƙƙin masu Sayen Kaya ta Nijeriya (FCCPC), Ondaje Ijagwu ya fitar a ranar Asabar.
Hukumar ta ce, ba za a janye shari’ar da ake yi da Meta ba duk da barazanar da ya yi.
FCCPC ta ce kamfanin ya yi barazanar ficewa daga Nijeriya ne domin a ji tausayinsa, da kuma matsawa hukumar canja matakin da ya ɗauka na cin tarar kamfanin.
Hakan kuma na zuwa ne bayan wani gargaɗi da Meta ya yi da farko cewa “za a tilasta masa rufe shafukan Facebook da Instagram a Nijeriya don kauce wa barazanar fuskantar hukunci”.
Hukumar ta zargi Meta da yi wa bayanan ’yan ƙasar kutse, ciki har da aika bayanan ba tare da izininsu ba da rashin mutunta masu amfani da shafukan kamar yadda ake yi a sauran ƙasashe da kuma ɓullo da tsare-tsare da ba su da kyau kan ’yan ƙasar.
A bara ne hukumomin sanya ido uku na Nijeriya suka lafta wa kamfanin tarar da ta kai fiye da dala miliyan 290, bisa zargin kamfanin da karya wasu dokoki.
