Ingila ta ƙara taƙaita lokacin bizar karatu daga shekara biyu zuwa wata 18

Spread the love

Gwamnatin ƙasar Ingila ta sanar da rage tsawon lokacin izinin aikin bayan karatu (Graduate Route Visa) daga shekaru biyu zuwa watanni 18. Wannan mataki na daga cikin gyare-gyaren da gwamnati ke yi domin daƙile abinda ta kira da “cin hanci da karkatar da manufar shirin” a harkokin karatu, neman mafaka daga ƙasashen waje.

A cikin takardar tsarin shige da fice da aka fitar a ranar Litinin, Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta bayyana cewa “Shirin Graduate Route bai cika manufofinsa na farko ba kuma ya zama wata hanya da ake bi wajen samun aikin da ba a tallafa masa ba.” Sabbin dokokin za su sanya ƙarin tsaurarawa wajen samun aikin dindindin da kuma yancin kawo ‘yan uwa daga ƙasashen waje.

Haka kuma, an sanar da cewa kawai jami’o’in da suka cika ƙa’idojin da aka sabunta ne za su ci gaba da samun lasisin ɗaukar ɗaliban ƙasashen waje. Jami’o’in da aka samu da laifin karya alƙawurra ko rashin nasarar ɗalibai wajen samun aiki bayan karatu za su fuskanci hukunci.

By ukarofi