Ɗumamar yanayi ta kassara Afrika, inji Majalisar Ɗinkin Duniya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Hukumar Kula da Yanayi ta Majalisar Ɗinkin Duniya (WMO), ta yi gargaɗin cewa matsalolin ɗumamar yanayi da ayyukan ɗan-adam ke haifarwa, na haddasa aukuwar masifun da suka janyo ƙarancin abinci da ruwan sha, baya ga kassara tattalin arziƙin kasashe da dama a Nahiyar Afirka.

A rahoton da ta wallafa a farkon makon nan, WMO ta ce masifun da ta ambata sun yi ƙamari ne a cikin shekarar 2024, inda a tsakanin watannin Maris da Mayu, ambaliyar ruwa da zaftarewar ƙasa a dalilin saukar mamakon ruwan sama suka yi sanadin mutuwar ɗaruruwan mutane tare da wasu fiye da dubu 700 da suka rasa muhallansu a Kenya da Tanzania da Burundi da dai wasu sassan gabashin Afirka.

Rahoton na WMO ya ƙara da cewa, masifun ambaliyar ruwan da kuma fari na kan gaba wajen raba al’ummomi da muhallansu a sassan Afirka, kamar yadda RFI Hausa ta ruwaito.

Lamarin da ya sanya zuwa watan Nuwamban shekarar bara adadin ‘yan gudun hijirar da ke cikin nahiyar ya ninka sau shida idan aka kwatanta da abinda aka gani shekaru 15 da suka gabata.

Haka kuma a watan Fabarairun 2024 Cibiyar da ke fafutukar rage kaifin talauci a duniya da ke Amurka, CGD ta yi gargaɗin cewa fiye da mutane miliyan 200 a Afirka ka iya faɗawa cikin bala’in yunwa mai tsanani la’akari da yadda matsalolin ɗumamar yanayi suke kassara ayyukan noma.

A taƙaice, ƙwararrun gargaďi suka yi kan cewa ɗaukacin nahiyar ka iya tafka hasarar aƙalla kaso 18 cikin 100 na adadin amfanin gonar da ta ke samarwa a duk shekara.

By Babaji