CERSDOV da UNFPA sun haɗa Kai da shugabannin Gombe don yaƙi da cin zarafin mata

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe

An gudanar da wani taron wayar da kan al’umma na kwana biyu a Gombe domin yaƙi da cin zarafin mata (GBV), wanda cibiyar bincike da magance cin Zarafin Gida (CERSDOV) ta shirya tare da haɗin gwiwar UNFPA, da gwamnatin ƙasar Norway, da ma’aikatar harkokin mata ta Jihar Gombe.

Taron ya tara muhimman masu ruwa da tsaki, ciki har da kansiloli mata, ƙungiyoyin agaji, shugabannin gargajiya, da jami’an shari’a, domin haɗa ƙarfi wajen shawo kan matsalar GBV da ke ci gaba da yawaita a jihar, tare da ƙarfafa gwiwar masu fafutuka a matakin tushe.

A jawabinta na bude taron, Kwamishiniyar harkokin mata, Asma’u Muhammad Iganus, ta bayyana damuwa kan yadda matsalar GBV ta yi ƙamari a Gombe, inda ta ce alƙaluma sun nuna yawan aukuwar cin zarafi ya kai sama da kaso 80 cikin 100.

“Wannan kira ne ga dukkanmu,” in ji Asma’u. “Haɗin kai tsakanin masu ruwa da tsaki ya zama wajibi, domin ganin an yi wa waɗanda abin ya shafa adalci tare da gina Jihar Gombe.”

Ta buƙaci mahalarta taron, musamman kansiloli mata, da su zama jagorori wajen isar da saƙon wannan taron ga al’ummomin su. Ta kuma nuna godiya ga CERSDOV, UNFPA, da gwamnatin Norway kan jajircewarsu wajen yaƙi da cin zarafin mata a Gombe.

Shugabar CERSDOV, Farfesa Hauwa’u Evelyn Yusuf, wadda kuma farfesa ce a fannin bincike kan laifuka da nazarin jinsi a Jami’ar Kaduna, ta gabatar da bayani kan mahimmancin fahimtar cin zarafin Mata da illolinsa.

“Cin zarafi ba ya tsaya kan duka kawai bane ya shafi zalunci da fyaɗe, da kuma nuna bambanci irin na jinsi,” in ji Farfesa Hauwa’u.

Ta bayyana cewa maza ma na iya fuskantar cin zarafin jinsi tare da jaddada mahimmancin fahimtar wahalhalun da waɗanda abin ya shafa ke ciki.

Da yake wakiltar Mai Kaltungo, Injiniya Saleh Muhammad, Magajin Gari, ya yaba wa wannan taro da ya mai da hankali kan wayar da kai game da matsalolin fyaɗe, musamman ga ƙananan yara.

“Wannan lokaci ne da iyaye za su sanya ido kan ‘ya’yansu tare da buɗe hanyoyin sadarwa a tsakaninsu,” in ji shi.

Haka zalika, babban hakimin cikin garin Gombe, wanda Sammani Bappah Yerima ya wakilta, ya yi nuni da rawar da shugabannin gargajiya ke takawa wajen magance matsalar cin zarafi da tabbatar da adalci.

Barrista Na’omi Abdu, wadda ta wakilci Ma’aikatar Shari’a, ta tabbatar wa mahalarta taron cewa ma’aikatar za ta ci gaba da tabbatar da cewa an hukunta waɗanda ake zargi da aikata cin zarafin ta hanyar fyaɗe.

“Ba za mu yi ƙasa a gwiwa ba wajen ganin an samu adalci,” ta jaddada, tare da yabawa lauyoyi kan jajircewarsu wajen shari’o’in cin zarafin jinsi.

Haka nan, Kansila Aishatu Buba daga ƙaramar hukumar Akko, ta bayyana taron a matsayin abin koyi kuma ta yi alƙawarin haɗa kai da shugabannin ƙananan hukumomi domin isar da saƙon a yankunansu.

“Wannan taron ya ƙara mana ƙwarin gwiwa. Tare zamu yi aiki tuƙuru don yaɗa wannan saƙon a dukkan al’ummominmu,” in ji ta.

By ukarofi