
Daga BELLO A. BABAJI
Rundunar ƴan sanda a Jihar Kaduna, ta yi nasarar kama barayin dabbobi guda biyu da kwato shanu 273 da ake zargin na wasu sanannun jagororin ƴan bindiga ne da ke ayyukansu a Kudancin jihar.
Lamarin ya biyo bayan atisayen haďaka da aka gudanar tsakanin ƴan sanda da sojoji da ƴan bijilante, sakamakon samun bayanan sirri na sace dabbobi a Kananan Hukumomin Kauru, Kaura da Kachia a jihar.
Bayanan sun nuna cewa, bayan sace dabbobin ne sai aka tafi da su yankin gabashin Akilibu da Dajin Rijana.
A ranar 11 ga watan Mayu ne aka kama wani mai suna Tanimu Ibrahim da Bello Musa a yankin Ishau dake Karamar Hukumar Faikoro a Jihar Neja bisa hannua laifin.
Kakakin ƴan sandan Kaduna, DSP Mansir Hassan a wata sanarwa, ya ce babban jami’in cibiyar yaki da laifukan garkuwa, CSP Sani Zuntu shi ne wanda ya jagoranci atisayen tare da kamo masu laifin.
