Filato: Sojoji sun kashe ƴan bindiga biyu a Wase

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Dakarun atisayen Operation Safe Haven (OPSH) a Jihar Filato, sun halaka wasu mutun biyu da ake zargin ƴan bindiga ne a Gundumar Gimbi dake Karamar Hukumar Wase.

Jami’in Hulďa da Jama’a na tawagar, Manjo Samson Zhakom ya faďi hakan a wata takarda da ya fitar a Jos, ranar Juma’a.

Ya ce, an kashe mutane biyun ne bayan samun rahoton ayyukan ƴan bindiga a yankin.

Manjo Zhakom ya kuma ce sojojin sun yi nasarar kwato wata bindiga kirar AK-47 a yayin atisayen.

Ya kirayi al’ummar jihar da su cigaba da ba su goyon a kokarinsu na dakile ayyukan ta’addanci a jihar, kamaryaddakamfanindillancinlabarai, NAN ya ruwaito.

By Babaji