
Daga BELLO A. BABAJI
Shugaba Bola Tinubu ya kaddamar da jirage biyu masu tashin angulu na kai farmaki domin karfafa ayyukan dakile matsalolin rashin tsaro a Nijeriya.
Taron kaddamarwar ya kuma yi daidai da cikar rundunar sojojin sama shekaru 61 da kafuwa, wanda aka gudanar a Abuja, inda Shugaban ƙasar ya samu wakilcin mataimakinsa, Kashim Shettima.
An kaddamar da sabbin jiragen ne ga dakarun sojojin sama tare da sanya musu lambobin NAF544 da NAF545, waɗanda aka samar domin karfafa ayyukan sojojin a yaki da ta’addanci.
Hakan wani bangare ne na habaka ayyukan sojoji da Gwamnatin Tarayya ke yi wajen samar da kayan yaki na zamani a gare su.
Da ya ke jawabi a taron, Shugaban sojojin, Air Marshal Hassan Abubakar ya ce, NAF za ta samu karin jiragen sama guda 49 zuwa nan da shekarar 2027.
Ya ce, guda tara daga ciki sun samu isowa tun a shekarar 2024 waɗanda suka haďa da helkwaftoci huďu kirar T-129, da jiragen leķen asiri uku na Air 360 da wasu helikwafta biyu na bin diddigi samfurin Agusta 109 Trekker.
Ya ƙara da cewa, hakan wani bangare ne na kokarin Shugaba Tinubu game da inganta harkar tsaro a Nijeriya, yana mai cewa za su tabbatar da amfani da kayan aikin bisa hanyoyin da suka dace wajen dakile ta’addanci a ƙasar.
