Najeriya ta yaba da irin gudummawar da EU ke bayarwa wajen sauya tattalin arzikin ƙasar – Shettima

Spread the love

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima,ya buƙaci Ƙungiyar Tarayyar Turai (EU) da ƙasashen Afirka da su haɗa kai domin ciyar da nahiyar gaba ta fuskar cigaba mai ɗorewa.

Shettima ya bayyana hakane yayin ganawar sa da jakadan EU a Najeriya da ECOWAS, Ambasada Gautier Mignot wanda ya gudana a fadar shugaban ƙasa dake Abuja,yana mai jaddada buƙatar ƙarfafa dangantaka tsakanin Najeriya da EU,inda yace lokaci ya yi da wannan dangantaka za ta aiwatar da abubuwan da za su kawo sauyi ta fuskoki da dama.

kana ya kuma bayyana EU a matsayin abokiyar haɗin gwiwar Najeriya, yana mai yabawa da irin gudummawar da take bayarwa wajen sauya tattalin arziki a mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Ya kuma tabbatar da cewa Najeriya za ta cigaba da amfani da damar da ke cikin shirin Global Gateway na EU, wanda ke zuba jari a ɓangaran ababen more rayuwa, kamar wutar lantarki sabbin hanyoyi,filayen sama da na Ƙasa, harma da cibiyoyin koyar da sana’o’i.

Ya kuma ce zuwa shekarar 2022, EU ta zuba jarin biliyan 309 a Afirka fiye da Amurka da China,inda ya tabbatar da ci gaba da goyon bayan shirin haɗin gwiwar “Joint Vision for 2030” da ke da nufin daidaita manufofin EU da Afirka bisa tsarin cigaban Afrika na 2063 tare da ƙoƙarin aiwatar da kasuwar cinikayya ta bai ɗaya ta Nahiyar Afirka (AfCFTA).

A wani labarin Kuma,

Mataimakiin Shugaban ƙasa Sanata Shettima yace Najeriya da Zambia suna da dangantaka mai ƙarfi tun shekaru da dama,kuma gwamnatin Tinubu na da niyyar ƙarfafa wannan zumunci.

Shettima ya bayyana haka ne lokacin da ya karɓi baƙuncin wakili na musamman ga Shugaban ƙasar Zambia, Hakainde Hichilema Dr Samuel Miambo, wanda ya ziyarci Najeriya don isar da saƙon gaisuwar Hakainde zuwa Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Shettima ya yabawa Zambia bisa gudummawarta a lokacin yaƙin neman ‘yancin Afirka daga mulkin wariyar launin fata, da kuma cigaban tsarin dimokuraɗiyya.

By ukarofi