‘Yan sanda sun kama wani matashi kan zargin kashe saurayin ƙanwarsa a Kano

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce ta kama wani matashi bisa zargin kashe saurayin ƙanwarsa a lokacin da ya je zance gidansa.

Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar ya ce lamarin ya faru ne a ƙauyen Kunya da ke yankin ƙaramar hukumar Minjibir.

Sanarwar ‘yan sandan ta ce matashin wanda ɗan asalin ƙauyen Goda, ya je Kunya ne wajen budurwarsa domin zance, sai dai jim kaɗan bayan zuwan nasa sai aka yi zargin cewa yayan budurwar mai suna Mansur Umar mai shekara 25 ya doke shi da sanda a ka, lamarin da ya haddasa masa munanan raunuka.

”Tuni aka garzaya da shi asibitin Kunya daga baya kuma aka mayar da shi asibitin Murtala domin ba shi kulawar gaggawa, inda daga baya aka tabbatar da mutuwarsa”, a cewar ‘yan sandan.

‘Yan sanda sun ce tuni suka kama Mansur, domin gudanar da bincike a sashen binciken manyan laifuka na rundunar ‘yan sandan jihar.

Rundunar ‘yan sandan ta yi kira ga jama’a su riƙa sanya haƙuri a cikin al’amuransu, tare da kai rahoton duk wata jayayya da aka samu tsakanin wasu mutane zuwa ofishin ‘yan sanda mafi kusa.

By ukarofi