Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
NAHCON ta ƙaddamar da sabuwar manhaja, yayin da ta bayyana jigilar maniyyata 14,165 a sawu 35 cikin kwanaki 6.
Domin sama wa maniyyatan Nijeriya sauƙi a aikin Hajji na bana, hukumar Alhazai ta ƙasa NAHCON, ta ƙaddamar da manhaja da ke ƙunshe da bayanai game da aikin Hajji kacokan ɗinsa.
Manhajar wanda jami’in hukumar Shafii Sani Mohammed ya bada bayanan abin da ya ƙunsa da kuma yadda za a sane shiya ce, manhajar na da sauƙin amfani sannan yana ƙunshe da bayanai da za su yi wa Alhaji amfani matuka a lokacin aikin Hajji.
Yayin da Manhaja ta tsunduma cikin wannan manhaja, ta gano cewa, aba ce da za ta yi wa maniyyaci amfani matuƙa.
Manhajar na ƙunshe da bayanai a manyan harsunan Nijeriya, Hausa, Igbo, Yoruba da kuma Turanci.
A cikin kowannensu akwai isassun bayanai game da aikin Hajji, masaukai, yadda za ka gane inda ka fito da inda ka dosa da dai sauransu.
Wannan wani cigaba ne da aka samu a aikin Hajjin bana.
Hakazalika, zuwa yanzu an yi jigilar maniyyata 13,781 zuwa Laraba, kamar yadda Hukumar NAHCON ta bada bayanai.
Hukumar ta ce a cikin kwanaki shida kacal ta kwashe maniyyata sama da 13,000 a sawu 34 zuwa Azahar ɗin ranar Laraba.
Bayan haka, tuni har ana fara kwashe maniyyatan Nijeriya daga Madina zuwa Makka, bayan kammala ziyara da suka yi a Madina.
A na sa ran sama da maniyyata 63,000 ne za su yi aikin Hajji a bana inshAllah daga Nijeriya.
