Hukumar Kula da Harkokin Ruwa ta Nijeriya (NAƙF) tare da haɗin gwiwar sojojin ruwa na Nijeriya na shirin karɓar baƙuncin Babban Hafsan Sojin Ruwa (CNS) karo na 12 na gasar ninkaya ta ƙasa.
An shirya gudanar da gasar ne daga ranar 15 zuwa 19 ga Yuli, 2025, a Asaba, babban birnin jihar Delta.
Gasar kamar yadda masu shirya gasar suka ce, za a yi shi ne domin tantance fitattun ‘yan wasa da za su wakilci Nijeriya a wasu muhimman gasar da suka shafi ƙasa da ƙasa, da suka haɗa da wasannin matasa na Afirka da kuma ƙaramib gasar ninkaya ta duniya.
A cewar shugabar hukumar ta NAƙF, Misis Chinoye Daphey, yayin wani taron manema labarai a ranar Laraba, “Wannan gasa wani ginshiƙi ne na tsare-tsare na hukumar na tantance fitattun ‘yan wasan da za su wakilci Nijeriya a manyan wasannin ƙasa da ƙasa.”
Taron, inji ta, zai samu mahalarta daga sassan jihohi 36 da birnin tarayya, da suka haɗa da ’yan wasa daga jihohi, ƙungiyoyi, sojoji, dakarun soji, da cibiyoyin ilimi.
