Kebbi: ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da masu ibada a wani ƙauye

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A karo na biyu cikin kwana biyu, ƴan bindiga sun shiga wani ķauye a Karamar Hukumar Danko-Wasagu na Jihar Kebbi, inda suka yi garkuwa da wasu Kiristoci guda takwas da ke tsaka da ibada a cocin ķauyen Zagami.

Shugaban ķaramar hukumar, Hon. Hussaini Aliyu Bena ya tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labarai a Birnin Kebbi bayan ganawa da Gwamna Nasir Idris da jagororin hukumomin tsaro, ranar Litinin.

Ya bayyana cewa, masu ibadar suna gudanar da ayyukansu ne a cocin a lokacin da suka samu labari cewa ƴan bindigar sun shigo yankin.

Lamarin da ya sa suka jingine ibadar da ƙoƙarin tserewa domin neman mafaka, inda a yayin haka ne ƴan bindigar suka yi nasarar garkuwa da takwas daga cikinsu.

Tuni aka sanar da Gwamnan a matsayinsa na jagoran tsaro a jihar halin da ake ciki, inda ya kira taron jami’an tsaro na gaggawa tare da bada umarnin samar da sansanin sojoji a kauyen da abin ya faru.

Haka kuma ciyaman ɗin ya ce, gwamnan ya umarci a kafa sansanin ƴan sandan na musamman a ķauyukan Dan-Umaru da Mairairai don tsare rayuka da dukiyoyin al’umma.

A makon da ya gabata ne ƴan bindiga suka farmaki wasu ķauyuka a Karamar Hukumar tare da kashe manoma 15 da raunata wasu mutane uku.

By Babaji