
Daga BELLO A. BABAJI
Mai bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkar Tsaro (NSA), Mallam Nuhu Ribaɗu, ya ce Gwamnatin Tarayya da hukumomin tsaro sun yi nasarar daƙile kaso mai girma na ayyukan ta’addancin da gwamnatin Bola Tinubu ta gada.
Ya bayyana cewa, an samu nasarar kawo ƙarshen kisan kiyashi da ɗaiɗaita dukiyoyi da harin ƴan ta’adda akan kadarorin gwamnati ta hanyar haɗaka tsakanin hukumomin tsaro.
A lokacin da ya ke magana a taron ƙasa na jiga-jigan Jam’iyyar APC a Abuja, yayin cikar Shugaba Tinubu shekaru biyu akan mulki, Ribaɗu ya ce gwamnatin ta gaji manyan rikici guda biyar a faɗin ƙasar.
Daga cikinsu akwai Boko Haram a Arewa ta Gabas da ɓarayin daji a Arewa ta Yamma da ƴan fafutukar raba ƙasa daga ƴan IPOB/ESN a Kudu masu Gabas da rikicin Neja-Delta gami da rikicin ƙabilanci ko tsakanin makiyaya da manoma a yankin Arewa ta Tsakiya.
NSA’n ya ƙara da cewa, gabannin shekarar 2023, sama da mutane 35,000 da 12,000 ne rikicin Boko Haram da ayyukan ƴan bindiga ya shafa, yayin da aka raba miliyoyi da muhallansu a yankunan da lamarin ya shafa.
Ya ce, sama da mayaƙan Boko Haram guda 13,543 ne aka kashe a shekara biyu tare da ķwato makamai sama da 11,000 da ɗaiɗaita ƴan ta’addar.
Haka kuma, ya bayyana cewa, kimanin ƴan Boko Haram 124,408 da iyalansu ne suka ajiye makamansu ga sojoji tun zuwan gwamnatin, inda kuma duk da kalubalen da ake fuskanta, ana cigaba da gudanar da atisaye a yankin ‘Tumbuktu Triangle’ da Tsibirin Tumbu domin farauto mayaƙan.
Har’ilayau, Ribaɗu ya ce hukumomin tsaro sun yi aiki tare wajen magance matsalolin Kudu maso Gabas da na lalata tashoshin mai a Neja-Delta.
