ICPC ta bankaɗo asusun da ’yan Nijeriya ke amfani da su wajen biyan digirin mako shida

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa mai zaman kanta (ICPC), Dakta Musa Adamu Aliyu a ranar Talata ya bayyana cewa hukumar ta gano wani asusu da wani ɗan ƙasar waje ya buɗe domin karɓar kuɗaɗe daga ‘yan Nijeriya da ke neman digiri na tsawon makonni shida a ƙasashen waje.

Shugaban ICPC ya bayyana haka ne a Abuja yayin wani taron bayar da shawarwari na masu ruwa da tsaki kan gano kadarorin, dawo da su, da gudanar da ayyukan cibiyar fayyace kuɗaɗe da mutuncin jama’a (CeFTPI) tare da goyon bayan ƙungiyar ‘Inter-Goɓernmental Action Group against Money Laundering’ a Afirka ta Yamma (GIABA).

Aliyu ya ce: “A cikin ‘yan makonni, mun gano cewa wani baƙo ya buɗe asusu a Nijeriya yayin da ɗaliban Nijeriya ke biyan kuɗi a cikin asusun domin samun wannan digiri na sati shida, kuma mun sami damar bin diddigin asusun.

“Mun samu umarnin kwace asusun, mun yi ƙoƙarin yin iyakacin ƙoƙarinmu don ganin an gurfanar da waɗanda suka aikata laifin.”

Ya kuma jaddada buƙatar dukkanin hukumomin cin hanci da rashawa da sauran hukumomin ƙasar nan su haɗa hannu tare da haɗin gwiwa domin ganin waɗanda ke aikata cin hanci da rashawa ba su amfana da laifukan da suke aikatawa ba.

“Mun yi ta ƙoƙarin ganin yadda za mu haɗa kai domin ganin mun kwato kadarorin da suka wuce yankin na Afirka, domin kamar yadda muka sani, Afirka ta sha fama da wannan matsalar ta rashin kuɗi ta haramtacciyar hanya.

“Haka zalika, idan za a iya tunawa, za mu tuna cewa tun lokacin da ake bautar da ƙasar Afirka ta Kudu na asarar ɗimbin albarkatu, mun san inda waɗannan kadarorin suka dosa, amma sun ci gaba da bayyana mana cewa kana da ƙalubale na cin hanci da rashawa.

“Amma batun shi ne wanda abin ya shafa ana zargin mu, muna fama da cin hanci da rashawa, amma suna ci gaba da zarge mu, shi ya sa a matakin yanki yanzu muke ƙoƙarin ganin yadda za mu haɗa kai don ganin mun farfaɗo, ganowa, mu maido da dukiyoyin zuwa nahiyarmu tamu.”

A jawabinsa na buɗe taron, Babban Darakta na CeFTPI, Umar Yakubu, ya bayyana cewa, taron ya tattaro muhimman masu ruwa da tsaki daga cibiyoyin yaƙi da cin hanci da rashawa, da jami’an tsaro, da ɓangaren shari’a, da ƙungiyoyin farar hula, da kuma abokan ci gaban ƙasa da ƙasa, domin lalubo hanyoyin haɗin gwiwa wajen kwato kadarorinsu da ƙaddamar da sabbin hanyoyin da za su taimaka wajen tabbatar da gaskiya da riƙo amanar ‘yan ƙasa.

By ukarofi