Jakadan Amurka a Isra’ila, Mike Huckabee, ya fito fili ya nuna fushinsa kan yadda ƙasashen Turai, musamman Faransa, Kanada da Birtaniya, ke sukar matakin soja da Isra’ila ke ɗauka a Gaza. A cewarsa, “ƙasashen nan sun ɗauki ɓangare suna dora laifi kan Isra’ila ba tare da nazarin ainihin yadda lamarin ya samo asali ba.”
Huckabee ya ce, ƙasashen da suka ɗaure wa Iran gindi a lokacin da take ƙoƙarin ƙirƙirar makaman nukiliya su ne yanzu ke la’antar Isra’ila da ke kare kanta daga makiyan da ke ƙaddamar da makamai masu linzami a kan biranenta. Wannan kalaman sun haifar da ƙarin ‘yar tsama a tsakanin ƙasashen yamma da Amurka, inda wasu ƙasashe ke kiran da a gudanar da bincike na ƙasa da ƙasa kan ɗanyen aikin soji da ake yi a Gaza.
