Kotun ƙoli ta kori ƙarar jihohi 36 kan kadarorin da aka karɓo daga ɓarayin gwamnati

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Kotun Ƙoli ta Najeriya ta kori ƙarar da gwamnoni 36 na tarayya da ƙungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) suka shigar, inda suka ƙalubalanci gwamnatin tarayya kan yadda take amfani da kuɗaɗen da aka karɓo daga ɓarayin gwamnati tun daga shekarar 2015 zuwa 2021.

A hukuncin da kwamitin alƙalai bakwai suka yanke, kotun ta ce ba daidai bane a kawo irin wannan ƙara kai tsaye gaban kotun ƙoli. Alƙalin kotun, Mai shari’a Mohammed Idris, wanda ya karanta hukuncin da Mai shari’a Chidiebere Uwa ya rubuta, ya ce ƙarar ta wuce iyakar hurumin kotun ƙoli, kuma kamata yayi a kai ta kotun tarayya.

A cikin ƙarar, jihohin sun bayyana cewa gwamnatin tarayya ta karɓo kuɗi har naira tiriliyan 1.8 da kadarori daban-daban kamar gidaje 167, motoci 450, manyan motoci 300 da gangar ɗanyen mai miliyan 20, amma ta kasa mayar da kuɗin cikin asusun tarayya kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

Gwamnonin sun ce gwamnatin tarayya ta karkatar da kuɗaɗen zuwa asusun tara Kuɗaɗen haraji da wasu asusun da ba su da tushe a tsarin mulki. Haka zalika, sun ƙalubalanci kafa wasu sabbin asusu da ake kiran ‘Asset Recovery Account’ da ‘Interim Forfeiture Recovery Account’, suna masu cewa hakan ya saɓawa tsarin kundin tsarin mulki.

Sun nemi kotun ƙoli ta umarci gwamnatin tarayya da ta dawo da dukkan kuɗin da aka karɓa daga 2015 zuwa yanzu cikin asusun tarayya domin a raba shi tsakanin gwamnati tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi.

Haka kuma, sun roƙi kotun ta tilasta gwamnati da hukumomin da abin ya shafa su bada cikakken bayani kan duk kadarorin da aka karɓa amma ba a mayar da su cikin asusun tarayya ba.

Sai dai kotun ƙoli ta ƙi karɓar buƙatun su, tana mai bayyana cewa irin wannan ƙara za ta dace a shigar da ita ne a kotun tarayya, ba kotun ƙoli ba.

By ukarofi