Ku kula da ƴan damfara, har yanzu ba a fara sayar da gidajen da aka ƙwace a hannun Emefiele ba – Gwamnatin Tarayya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Ma’aikatar Gine-gine da Raya Birane ta ce ba ta fara sayar da kowane sashi na rukunin gidaje guda 753 da aka ƙwace ba, wanda aka alaƙanta shi da tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele.

A sanarwar da Daraktan yaɗa labaranta, Badamasi Haiba ya fitar, Ma’aikatar ta ce kaɗai abinda ta yi shi ne karɓar iko da shi daga hannun hukumar EFCC a ƙarƙashin umarnin Shugaba Bola Tinubu.

Hakan ya biyo bayan samun labarin waɗansu ɓata-gari ne da ke karɓar kuɗi a hannu mutane da sunan sayar da wasu ɓangarori na rukunin gidajen.

Ya ce, ƴan damfarar suna karɓar kafin alkalami na N500,000 daga masu neman sayen gida a madadin ma’aikatar.

A madadin faɗa wa tarkon ƴan damfarar, Ministan Ma’aikatar, Ahmed Musa Ɗangiwa ya ce za a samar da kwamiti na musamman da zai yi aiki akan lamuran da suka shafi rukunin gidajen.

Ya ƙara da cewa, ma’aikatar za ta sanar da al’umma tsarin da za a bi wajen sayar da gidajen kamar yadda Shugaba Tinubu ya umarta.

Ya kuma kirayi al’umma da su kasance a ankare da masu damfarar gami da tuntuɓar ma’aikatar game da dukkan wani bayani da ya shafi lamarin.

Kazalika, jami’in ya ce ma’aikatar za ta cigaba da ƙoƙarin tabbatar gaskiya da adalci game da lamarin.

By Babaji