Sojojin sama sun tarwatsa haramtattun wuraren tace mai sama da 100 a wata biyar

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A wani yunƙuri na yaƙi da satar ɗanyen mai da lalata muhalli, Rundunar Sojojin Sama (NAF) ta tarwatsa haramtattun wuraren tace ɗanyen mai guda 100 a yankin Neja-Delta cikin watanni biyar da suka gabata.

A yayin atisayen sojojin sama ƙarƙashin dakarun ‘Operation DELTA SAFE’ (OPDS) aka samu nasarar daƙile manyan laifukan domin kare albarkatun mai daga shiga hannun ɓata-gari gami da tseratar da ƙashin bayan tattalin arziƙin Nijeriya daga faɗawa cikin mawuyacin hali.

Daraktan yaɗa labaran NAF, Ehimen Ejodame a wata takarda, ya bayyana cewa jami’an ‘115 Special Operations Group’ ne suka gudanar da atisayen, wanda ya nuna yadda NAF ke ƙoƙarin bai wa kadadorin ƙasa kariya daga masu yi musu zagon-ƙasa.

Ya ce, tsakanin watannin Janairu da Mayu 2025, ne dakarun suka gudanar da atisayen sama guda 173 da na ruwan boma-bomai guda 265, waɗanda suka shafe jimillar awanni 270 suna ƙaddamarwa.

Lamarin ya shafi jihohi masu albarkatun mai da suka haɗa da Ondo, Edo, Delta, Bayelsa, Ribas, Akwa-Ibom da Kuros-Riba.

Sanarwar ta kuma ce, atisayen ya yi sanadin tarwatsa kwale-kwale guda 53, tankokin dafawa 74, wajen ajiyar ɗanyen mai guda biyu da motoci da dama da ake amfani da su wajen safarar man da aka sace.

By Babaji