Wani da ake zargin ɗan ƙunar bakin wake ne ya mutu a Abuja

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Wani mutum da ake zargin ɗan ƙunar baƙin wake ne ya mutu kusa da Barikin Mogadishu da ke unguwar Asokoro, babban birnin tarayya Abuja.

A wani bidiyo da jaridar Manhaja ta gani, an ga gawar mutumin kwance a gefen wata katanga yayin da jami’an tsaro ɗauke da makamai suka kewaye wurin.

Wani rahoto daga gidan talabijin na AIT ya nuna cewa jami’an tsaro suna ci gaba da bincike a yankin.

Har yanzu ba a tabbatar da yadda mutumin ya mutu ba ko kuma wanene ke da alhakin hakan.

Ƙoƙarin da aka yi don jin ta bakin mai magana da yawun ‘yan sandan babban birnin tarayya, SP Josephine Adeh, bai yi nasara ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

By ukarofi