Saudiyya ta koro Sheikh Gumi bayan hana shi yin aikin hajjin bana

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Sanannen malamin addinin Musulunci a Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana cewa, hukumomin Saudiyya sun hana shi gudanar da aikin hajji duk da cewa yana da biza.

A wani saƙo daga shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, babban malamin ya ce yana ganin ra’ayoyinsa akan harkokin siyasar duniya sun taimaka wa hukumomin ɗaukar matakin akansa.

Ya ce, ya yi abinda ya ke wajibi akansa ta hanyar da aka shar’anta kuma tuni ya dawo gida Nijeriya, yana mai kafa hujja da ayar Al’ƙu’rani.

Sheikh Gumi ya kuma yaba wa hukumomin Nijeriya, waɗanda ya ce sun shiga tsakani domin warware matsalar.

Ya kuma yi godiya bisa damar da ya samu na mayar da hankali akan lafiyarsa da harkokin noma, yana mai kira ga ƴan Nijeriya da su yi addu’ar samun kariya ga dukkan maniyyata da ci-gaban Nijeriya.

By Babaji