Fusatattun matasa sun kashe DPO a Kano

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Rahotanni daga ƙaramar hukumar Rano a Jihar Kano sun tabbatar da tashin hankali bayan mutuwar wani matashi mai gyaran babur, Abdullahi Musa, wanda aka cafke bisa zargin tuƙin ganganci da shan kayan maye.

Rundunar ‘yan sandan Kano ta bayyana cewa Musa ya samu matsala da lafiyarsa yayin da yake tsare, kuma aka garzaya da shi asibitin Rano inda ya rasu da safiyar Litinin, 26 ga Mayu, 2025.

Bayan bazuwar labarin mutuwarsa, wasu matasa suka kai hari Ofishin ‘yan sanda na Rano, inda suka ƙone wani sashi na ofishin, suka lalata motoci guda goma da ƙona guda biyu.

Har ila yau, matasan sun raunata DPO na ofishin sosai, wanda daga bisani ya rasu a asibitin koyarwa na Aminu Kano inda aka garzaya da shi domin ceto rayuwarsa.

Rundunar ‘yan sanda ta kama mutane 27 da ake zargi da hannu a harin, yayin da kwamishinan ‘yan sanda na jihar, CP Ibrahim Bakori, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike. Ya kuma kai ziyara ta ta’aziyya ga Sarkin Rano, Alhaji Mohammed Isah Umar.

Rundunar ta buƙaci jama’a da su kwantar da hankalinsu tare da gujewa ɗaukar doka a hannunsu, tana mai tabbatar da cewa za a hukunta duk masu hannu a lamarin.

By ukarofi