Daga USMAN KAROFI
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da ci gaba da karɓar filaye 4,794 da aka soke mallaka a babban birnin tarayya (FCT) saboda rashin biyan kuɗin haya na ƙasa (Ground Rent) na tsawon shekaru. Wannan mataki ya biyo bayan matakin da ma’aikatar kula da filaye ta Abuja ta fara na kulle gine-gine da dama a ranar Litinin.
A cewar daraktan kula da harkokin filaye, Chijioke Nwankwoeze, gwamnati ta ba wa masu filayen sabuwar dama na makonni biyu don su biya bashin da a ke bin su, in ba haka ba za su rasa kadarorinsu.
Wannan umarni ya shafi filaye da kadarori da suka haɗa da na hukumomin gwamnati, kamfanoni da kuma na mutane masu zaman kansu a unguwanni irin su Maitama, Asokoro, Wuse, Garki da Guzape.
A sabon tsarin, masu kadarori a yankin Central Area za su biya tarar Naira miliyan biyar tare da bashin hayan ƙasa, yayin da masu filaye a yankunan Maitama, Asokoro, Wuse II da Guzape za su biya Naira miliyan uku. Yankunan Garki I, Garki II da Wuse I kuwa, za su biya tarar Naira miliyan biyu.
Haka kuma, an umarci duk wanda ya sayi fili daga wani mutum amma bai samu amincewar Minista ba ko kuma bai yi rijistar takardun mallaka ba, da su hanzarta yin hakan cikin kwanaki 14. Ministan babban birnin tarayya, Barrister Nyesom Wike, ya jaddada cewa gwamnati ba za ta yi sakaci da waɗanda ba sa biyan haƙƙoƙin da suka rataya a kansu ba. Ya buƙaci duk masu kadarori a Abuja da su tabbatar da cewa suna biyan dukkan kuɗaɗen da suka wajaba a kansu domin tabbatar da ci gaban birnin.
