Abuja: Sojoji sun tabbatar da tarwatsewar abin fashewa a Barikin Mogadishu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Rundunar Sojojin ƙasa ta tabbatar da rahoton tarwatsewar wani abin fashewa a barikin sojoji na Mogadishu dake birnin tarayya Abuja.

A sanarwar da ta fitar ta kafar X, ta ce lamarin ya auku ne a wajen tsayawar motoci dake daura da barikin.

Ta kuma ce, tuni aka ɗauki matakan da suka dace.

Rundunar ta ƙara da cewa, za ta fitar da sauran bayanai da zarar an kammala bincike.

By Babaji