Dubunnan yara ake haifa da cutar sida – NACA

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

A yayin bikin ranar yara ta duniya da aka gudanar a ranar 27 ga Mayu, 2025, Shugabar hukumar kula da cutar AIDS ta ƙasa (NACA), Dakta Temitope Ilori, ta bayyana cewa dubban jarirai a ke haihuwa ɗauke da ƙwayar cutar HIV wato sida a Najeriya duk shekara. Ta ce wannan lamari na daga cikin manyan ƙalubale masu matuƙar tada hankali, kasancewar cutar na iya hana yaran samun lafiya da makoma mai kyau.

Dakta Ilori ta jaddada cewa hanyoyin hana yaɗuwar cutar daga uwa zuwa jariri (PMTCT) na ɗaya daga cikin matakan da suka fi tasiri wajen daƙile yaɗuwar cutar sida a tsakanin yara. Ta ce idan aka tabbatar kowace mace mai ciki ta samu gwaji da wuri, kuma aka fara mata magani cikin lokaci, hakan zai hana yaɗa cutar zuwa jariri yayin ɗaukar ciki, haihuwa da kuma lokacin shayarwa.

Rahoton hukumar UNICEF na shekarar 2023 ya nuna cewa yankin Yammacin da Tsakiyar Afirka, ciki har da Najeriya, na ɗauke da kaso mai yawa na yara masu fama da cutar sida. Yankin na ɗauke da kashi 26 cikin 100 na yara masu ɗauke da cutar a duniya, inda kusan kashi 90 cikin 100 na sabbin kamuwa a tsakanin matasa, musamman mata, ke faruwa a yankin.

A ƙarshe, Dakta Ilori ta buƙaci a ƙara zage damtse wajen kare yara daga kamuwa da cututtuka da za a iya kauce wa. Ta ce ranar yara ta duniya wata dama ce da ke tunatar da mahimmancin kare lafiyar yara da tabbatar da makomar su, ta hanyar samar da kulawa da jinya ga mata masu ciki da suka kamu da sida.

By ukarofi