Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Shugaban kwamitin gabatar da taron ƙungiyar masu bada gilashin ƙara ganin ido a asibitocin Nijeriya da ake ƙira ANDO, wato Association of Nigerian Dispensing Opticians, Aliyu Alawo, ƙarƙashin shugabancin Opt Obote Syɓester Oghenerho, shugaban ƙaramin kwamitin aiwatar da taron na Kano ya bayyana cewa rashin tallafi da gwamnatin Kano ta yi musu alƙawari za ta bayar kuma bata bayar ba shi ne ya sa taron na ƙasa karo na 10 na farko a Arewa bai yi armashi ba kuma aka samu cikas, domin a cewarsa sun ta kaiws da komowa ana za a ba su amma ba su karɓa ba, domin ba su samu ba har ranar taron, a cewarsa saboda halin ‘yan siyasa na jeka ka dawo wannan shi ne dalili na farko da ya haddasa matsalar sukurkucewar taron a Kano, kamar dai yadda ya bayyana wa manema labarai a taron da aka gabatar a makon da ya gabata a Central Hotel Kano.
Haka kuma Alawo ya bayyana cewa dalili na biyu shi ne rashin goyon bayan shugabannin ƙungiyar ANDO ta ƙasa kamar yadda ya kamata domin a cewarsa ba su so a yi taron ba, don haka ba su bada abinda ya kamata taron ya yi armashi ba, “mu kuma muka yi amfani da abinda ya samu domin ba za mu ɗauki kuɗin aljihunmu mu yi amfani da shi ba kuma muna zargin basu so a kawo taron Arewa ba,” inji Aliyu Alawo shugaban ƙaramin kwamitin ANDO a Kano.
Shi kuwa magatakardar ƙungiyar ANDO na ƙasa Dr Obinna Edwin Aiwaka ya ce wannan ƙungiya tana yin taro duk shekara domin yaɗa ilimi a tsakanin manbobinta a kan wannan aiki na bada gilashin Ido a asibitoci ya bayyana wannan taro a matsayin abin jin daɗi kan irin yadda yaga Kano wajen zaman lafiya da kuma kyakyawar fahimta ta ke da shi da hukumomin ƙasar nan.
Shi kuwa Abdulsamad Ibrahim Ringim jigo ne a ANDO daga Jigawa takaicin sa ya bayyana kan yadda ɗalibai da sauran mahalarta taron suka shiga wani hali na rashin abinci wadatace a wurin taron duk da yake cewa a sauran taruruka ba haka abin yake ba don haka basu ji daɗi abin da ya faru ba kuma zasuyi iya ƙoƙarinsu na ganin baa maimaita irin wannan taro mara armashi ba domin wannan taro ya na da mahimmanci ga yan ƙungiyar domin sai kana halartar sa ne zaka samu damar cigaba da aiki a asibiti ko wata cibiyar lafiya kamar yadda yake a doka kuma ya yi fatan alkairi da addu’a ga ɗaukacin jagororin ƙungiyar na ƙasa da jihohin Nijeriya.
