Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Dimukraɗiyya dai kamar yadda masana suka ce, gwamnatin al’umma ce da al’ummar suka assasa ta hanyar zaɓe, sai dai a jihar Kebbi salon dimokuraɗiyya ya sha bamban da sauran wurare.
Al’umma dai suna zaɓen waɗansu mutane ne bisa ga zaton samun kyakykyawan shugabanci ko kuma wakilci don nemo musu waɗansu haƙƙoƙansu tun kama daga matakin ƙaramar hukuma zuwa jiha har zuwa gwamnatin tarayya.
Da alamu dai iskar guguwar siyasa ta soma kaɗawa ƙasar nan, sai dai irin iskar da ke kaɗawa a jihar Kebbi da alamu ta sha bamban da sauran jihohi duk da ya ke a ko’ina da irin yadda su ke ta su dambarwar da kuma yadda suke ta faman nemo bakin zaren don warwareta tun kama daga neman muƙamai zuwa neman samun fada a wajen shugaban ƙasa.
Jihar Kebbi dai ta daɗe tana fama da dambarwar siyasar cikin gida musamman saboda kasancewar jihar ta ‘yan boko, inda aƙalla kashi tamanin kowa ya dogara ne da gwamanti inda kuma adawa ba ta cika tasiri ba sai dai tana yi wa gwamnati barazana ne kurum sai an zo lokacin zaɓe sai ‘yan takarar jam’iyyun adawa ke shan mamaki in bayan da a baya-bayan nan da jam’iyyar adawa ta PDP ta ƙwaci waɗansu kujerun ‘yan majalisar dokoki, sai dai su ma bayan wani ɗan ƙaramin lokaci da shan rantsuwar kama aiki suka bijire suka bi gwamnatin APC da ke mulki ƙarƙashin jagorancin Malam Nasir Idris.
Wannan ya sanya yanzu jihar Kebbi da alamu ta kama hanyar zama mai jam’iyya ɗaya tilo, sai dai abu ɗaya zai iya zame mata tarnaƙi nan gaba kaɗan saboda waɗansu jiga-jigan siyasar jihar da ƙasa ma bakiɗaya suka dawo cikin Jam’iyyar ta APC bayan wani fushin zuciya da suka yi a shekarar 2023 lokacin da aka nemi cin zarafin su wajen zaɓen fitar da gwani don neman tsayawa takarar kujerar gwaman jihar tsakanin Sanata Dokta Yahaya Abdullah da kuma Malam Nasir Idris inda aka ce wai Sanata Yahaya Abdullahi wanda a lokacin yana shugaban masu rinjaye a zauren majalisar dattawa bai samu ƙuri’a ko ɗaya ba, wanda dalilin haka ne shi da Sanata Adamu Aliero da Garba Maidoki suka fice suka koma Jam’iyyar adawa ta PDP aka ba su dama kuma suka lashe zaɓe.
Bayan da tafiya ta yi tafiya ne Shugaban ƙasa Bola Tinubu saboda sanin muhimmancin waɗannan mutanen ya nemi su dawo jam’iyyar sa ta APC saboda su ƙarfafa masa ƙudurinsa na zarcewa a shekarar 2027 bayan kammala wa’adin mulkinsa na farko, bayan wata kiki-kaka daga ƙarshe dai suka amince kuma suka dawo Jam’iyyar APC ɗin.
Sai dai dawowar waɗannan mutanen Jam’iyyar APC bai yi wa waɗansu daɗi ba saboda yanzu haka an soma tayar da ƙura wacce ta ke ba ƙarama ba saboda tun a zaman farko an soma tayar da jijiyoyin wuya tsakanin waɗansu ɓangarorin jam’iyyar, da ya ke yanzu jam’iyyar ta APC ta kara kasuwa gidaje daban-daban da suka haɗa da ɓangaren tsohon Ministan Shari’a Abubakar Chika Malami da ɓangaren tsohon Gwama Sanata Atiku Bagudu da ɓangaren shi kan sa Gwamna Malam Nasir Idris sai kuma ɓangaren Sanata Adamu Aliero inda kowane ɓangaren kuma yana ƙoƙarin ganin ya riƙe kambun siyasar jihar ta Kebbi.
A baya-bayan nan a wani taro da aka gudanar na masu ruwa da tsaki a Jam’iyyar APC ta jihar Kebbi an yi tonon sili tsakanin Sanata mai wakiltar mazabar gundumar Kebbi ta tsakiya da kuma Sanata Atiku Bagudu waɗanda dukkan su tsofaffin gwamnonin jihar ne wanda abin ya nuna da alamu ya ruruta wutar ja in ja da ke tsakanin ɓangarorin da kowane ke ganin ya fi fada wajen Shugaban ƙasa Bola Tinubu.
Waɗannan ɓangarorin dai yanzu haka kowane ƙoƙarinsa duk bai wuce ya ga ya ƙwace kambun jagorancin siyasar jihar ba daga hannun Gwamna Malam Nasir Idris da ake ganin salon mulkin sa irin na yan uwa da abokai ne, yayin da a ɗaya ɓangaren kuma tsohon Ministan Shari’a Abubakar Chika Malami ya ja daga saboda a cewar magoyabayansa akwai wata yarjejeniya ta wa’adi ɗaya saboda shi ma dana inda ɗaya daga cikin shugabannin siyasar da ke goyon bayan gwamnatin jihar kuma shugaban hukumar Alhazan jihar Alhaji Musa Yaro Enabo ya ƙaryata wannan maganar tare da nuna yadda kowane gwamna ya yi wa’adi biyu shi ma sai ya yi.
Masana harkokin yau da kullum da wakilinmu ya tattara bayanai daga wajen su sun nuna cewa akwai yiyuwar rikicin cikin gida yana iya zama silar faɗuwar Jam’iyyar APC saboda rarrabuwar kai da ya addabi jam’iyyar wanda suka bayyana cewa yanzu haka dai a Jam’iyyar APC ta jihar Kebbi ta rarrabu gidaje daban-daban da suka haɗa da ɓangaren tsohon gwamna Adamu Aliero da ɓangaren tsohon Ministan Shari’a Abubakar Chika Malami da ɓangaren shi kan sa mai girmma gwamna Malam Nasir Idris wanda a cikin sa shi ma akwai rarrabuwar kai kuma kowane bayan yana da ƙarfi kuma yana da’awar idan bai samu biyan buƙatarsa ba to ba shakka zai bi Jam’iyyar haɗaka saboda haka ita kan ta Jam’iyyar APC ta karɓi mulki.
A ɗaya ɓangaren kuma daga cikin jiga-jigan siyasar da ke ɓangaren Honarabul Shehu Koko tsohon ɗan majalisar wakilai da wakilci ƙananan hukumomin Koko da Maiyama da aka kora daga Jam’iyyar da ya ƙi a bayyana sunansa ya tabbatar da ƙudurin su na ba za fice daga jam’iyyar ba har sai sun ga abinda ya ture wa Buzu naɗi saboda an tarar da su a cikin jam’iyyar ne ba shigowa suka yi ba.
Ya ƙara da cewa ba da jam’iyyar ne su ke da matsala ba illa dai akwai hasashen tsohon gwamnan jihar ne Sanata Atiku Bagudu ne ke ganin da su aka kitsa aka kayar da shi a zaɓen da ya gabata na shekarar 2023 da ya nemi kujerar ɗan majalisar dattawa saboda haka shi ma yanzu ya ke neman fansa saboda Shehu Koko ya nuna ra’ayinsa na neman wannan kujerar.
Sai dai yanzu dai samun nasarar karɓuwar Jam’iyyar APC a Jihar Kebbi ya ta’allaƙa ne da abin da zai faru bayan an kammala tsayar da ‘yan takara a jihar saboda da yawancin jagororin ‘yan siyasa da ke da magoyabaya suna ganin an mayarda su saniyar ware haka-zalika wadanda ke rike da madafun iko sun juya musu baya ba wani sai dai kawai suna tarawa kawunan su kudi da yayan su yayin da wadansu kuma ke kokawa da cewa a jihar Kebbi ne kaɗai mawaƙin siyasa zai zo biki ya samu sama da motoci goma da kuma ɗaruruwan milliyoyi yayin da ma’aikatan gwamanti da ‘yan siyasa ke neman na sakawa a bakin salati.
