Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Cibiyar bincike ta haɗin guiwa (JIC) ta ce akwai ‘yan ta’adda 1,450 da ke jiran a yanke musu hukunci.
Muƙaddashin kwamandan JIC, AU Ahmed, wanda ya samu wakilcin Olugbenga Adeniyi, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake ganawa da manema labarai kan ayyukan cibiyar a Maiduguri.
Ahmed wanda soja ne mai muƙamin kanal ya ce, ‘yan ta’adda 1,450 na daga cikin ‘yan ta’adda 1,877 da aka kama da cibiyar ke bincike a kan yadda suka shiga ayyukan ta’addanci.
Ya ce bayan kammala bincike an ware waɗanda aka kai su domin sabunta tunaninsu a yayin da wasu aka kai su cibiyar Giwa da ke a cikin ‘yan ta’addan an kai su Kainji domin fuskantar shari’a.
“Bayan binciken, sashen kula da ƙararraki (CCG) ya yi nazarin binciken tare da ba da shawara irin ta masana shari’a a kansa.”
“La’akari da sakamakon binciken da kuma shawarar masana shari’a, an karkasa waɗanda ake tsare da su zuwa gida uku; waɗanda za a yanke wa hukunci, waɗanda za a sabunta musu tunani da waɗanda za a sake mayar da su cikin al’umma.”
“Waɗanda aka ba da shawarar a yanke musu hukunci an kai su Giwa da ke Kainji. Su kuma rukunin da za a mayar cikin al’umma an miƙa su ga gwamnatin jihar Borno,” inji shi.
Kwamandan ya bayyana rashin samun shaidu a matsayin dalilin da ya kawo tsaiko wajen gudanar da ayyukan ƙungiyar yana mai cewa suna shan wahala wajen samun shaidu.
Sannan ya koka kan jinkiri sa ake samu na yanke ‘yan ta’addan hukunci bayan kammala bincike a kansu.
“Wannan cibiya na shan wahala wajen samun shaidu da za su tallafa wa bincikenta.”
“Wannan kuma na da alaƙa ne da rashin samun kutsawa wuraren da aka aikata laifukan, da tsoron ba sa shaida daga wajen al’umma.”
“Haka ma rashin zartar da hukunci bayan kammala bincike yana kawo wa wannan cibiya tsaiko.”
“Mafi yawan waɗanda ke tsare suna jiran hukunci ne. Sai dai jan ƙafa da ake samu wajen yanke hukuncin ne ke ƙara tsawaita wa’adin ɗaurarrun,” ya bayyana.
Kamfanin Dillancin Labarai na ƙasa (NAN) ta bayyana cewa an sha samun kiraye-kiraye na samar da kotuna na musamman da za su riƙa yanke hukunci kan laifuka da suka shafi ta’addanci.
