‘Yan sanda suka kashe ƙanwata ba ‘yan bindiga ba – Gwamnan Taraba

Spread the love

Gwamnan Jihar Taraba, Kefas Agbu, ya bayyana cewa ɗan sanda daga cikin tawagar tsaron mahaifiyarsa ne ya harbe ‘yar uwarsa, Atsi Kefas, a hanyar Wukari zuwa Chinkai a shekarar 2024. Wannan ya saɓawa rahotannin da suka ce ‘yan bindiga ne suka kai hari da nufin yin garkuwa da su. Gwamna Kefas ya bayyana haka ne yayin ganawa da manema labarai a birnin Jalingo, inda ya ce bincike ya tabbatar cewa harbin da ya kashe Atsi an yi shi ne daga nesa kaɗan.

Gwamnan ya ƙara da cewa, an samu harsashi a jikin Atsi yayin tiyata, wanda hakan ya tabbatar da cewar ɗan sandan da ke cikin motar tare da su ne ya aikata kisan. Yayin da yake tuna marigayiyar Atsi, ya kuma yi addu’a ga sama da mutane 50 da suka rasa rayukansu a harin da aka kai a ƙaramar hukumar Karim-Lamido a jihar. Ya buƙaci jama’a su zauna lafiya da juna domin kaucewa rikice-rikice da ke janyo asarar rayuka.

A ƙarshe, gwamna Kefas ya bayyana cewa gwamnati za ta kafa kwamitin bincike domin gano musabbabin rikicin da ya faru a yankin Karim-Lamido, tare da samar da zaman lafiya mai ɗorewa. Har yanzu rundunar ‘yan sandan jihar Taraba ba ta fitar da wata sanarwa kan zargin da gwamnan ya yi ba.

By ukarofi