Fadar Shugaban Ƙasa ta yi wa Atiku martani bisa kalamansa na sukar gwamnati

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Kakakin Shugaban Ƙasa, Bayo Onanuga ya soki tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar bisa kalamansa akan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana mai bayyana su a matsayin na kai-da-kai ba don ƙasar ba.

A lokacin da ya ke magana kan zargin gwamnati da aiwatar da tsare-tsare da suka ci karo da buƙatun al’umma da Atiku ya yi, Onanuga ya ce yana da muhimmanci tsohon shugaban ƙasar ya sani cewa gwamnatin ta cimma nasarori da dama a tsawon shekaru biyu na mulkinta.

Ya ce, gyare-gyaren da Tinubu ke yi kamar cire tallafin fetur da daidaita matakin canjin kuɗaɗen waje, matakai ne da gwamnatocin baya suka gaza cimmawa, waɗanda daga ciki har da na Obasanjo da Atiku.

Ya kuma ce, a lokacin yaƙin neman zaɓe, Tinubu bai yi alķawarin sauye-sauyen za su zo da sauƙi ba, saidai ababe ne da suke da muhimmanci wajen ceto ƙasar daga rugujewa.

Onanuga ya kuma kare alƙiblar tattalin arziƙi na gwamnatin, inda ya ce tsare-tsaren ɓangaren sun taimaka wajen daidaita al’amarun kuɗaɗen ƙasa da rage rashawa.

Haka kuma ya yi watsi da cewa gwamnatin ba ta kula da walwalar al’umma, inda ya ce ta samar da shirin bada lamunin kuɗin karatu ga ɗalibai, wato NELFUND, wanda a ƙarƙashinsa kimanin ɗaliban Nijeriya guda 600,000 sun amfana.

Kazalika, ya zargi Atiku da dogara da labaran ƙarya da ake yaɗawa a Soshiyal Mediya na cewa gwamnatin Tinubu tana karɓo aron kuɗi ga kasafin 2025, batun da ministan kuɗi ya ƙaryata, yana mai cewa Dala biliyan 1.2 kaɗai gwamnati ta nufi arowa a wannan shekarar.

By Babaji