Osimhen ya bayyana kulob ɗin da ba zai taɓa zuwa ba

Spread the love

Ɗan wasan gaba na Super Eagles, Victor Osimhen, ya bayyana cewa zai fi so ya cigaba da zama a Galatasaray fiye da komawa Juventus. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta danganta shi da komawar zuwa tsohuwar zakarun Serie A, duk da yana kan aro daga Napoli zuwa Galatasaray.

Wani masani daga kulob din Galatasaray, Yakup Çınar, ya ce Osimhen ya nuna rashin sha’awar komawa Italiya, inda ya ce: “Juventus na son Osimhen, amma ya ce zai fi son zama a Galatasaray.” Ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi a tashar YouTube ta Yeni Açık, kamar yadda jaridar habersarikirmizi ta rawaito.

Ko da yake babu tabbas kan makomarsa, ana hasashen cewa Osimhen zai bar Istanbul a wannan kakar, inda ake danganta shi da komawa ƙasashen Saudiya ko Ingila. Çınar ya ce ƙungiyoyi daga ƙasar Saudi Pro League sun yi masa tayi mai tsoka, sai dai har yanzu bai yanke hukunci na ƙarshe tare da Galatasaray ba.

By ukarofi