Abinda ya sa na ƙi zaɓar Tinubu da yi masa aiki – Amaechi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Tsohon Gwamnan jihar Ribas kuma Ministan Sufuri sau biyu, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa ya ƙi zaɓe ko aiki wa Shugaba Bola Tinubu ne saboda ya gamsu cewa ba zai jagoranci Nijeriya ba.

Amaechi ya bayyana hakan ne a yayin lakcar bikin cikarsa shekaru 60 a duniya, wanda aka yi a Abuja inda ya ce ya haɗu Tibubu a Yola, sai ya ce masa “ba zan yi ma ka aiki ba kuma ba zan zaɓe ka ba.”

Ya ce, mutane suna cewa bai yi wa jam’iyyar APC ko PDP aiki ba, wanda ya ce hakan ya faru ne a sakamakon ya gamsu cewa akwai matsalar kamala a duka ɓangarorin.

Ya kuma ce, a Nijeriya ne a yau ƴan ƙasa da dama suke yin zaɓe domin addini da ƙabilanci inda ake yaudarar al’umma saboda rashin sanin inda suka dosa.

“Bari na faɗa muku, babu wani shugaban Nijeriya da ya damu da talakawa, domin sun san cewa ƴan Nijeriya ba za su iya yi musu komai a yayin da suka samu mulki. A lokacin da ƴan Nijeriya suka yi zanga-zanga, Shugaban ƙasar ya sanar da ƙarin farashin fetur saboda sun san ba za ku iya yin komai ba”, inji tsohon gwamnan.

Ameachi ya ƙara da cewa, babban abinda ke damun sa shine yadda za’a ciyar da Nijeriya gaba da ilimantar da al’umma akan sanin ciwon kansu ta yaddaza su san abinda ya ke na daidaida akasin haka domin zama ƴan ƙasa na gari da zaɓar shuwagabannin masu nagarta.

By Babaji