Wakilan Kano 21 ne suka rasu a hanyarsu ta dawowa gasar wasanni ta ƙasa

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Aƙalla mutane 21 ne aka tabbatar da rasuwar su a sakamakon wani mummunan haɗari da ya ritsa da wakilan Jihar Kano a tawagar gasar wasanni ta ƙasa.

Lamarin ya faru ne a safiyar yau Asabar a garin Dakatsalle na ƙaramar hukumar Kura dake Kano, a dai-dai lokacin da suke kan hanyar su ta dawowa gida, kamar yadda ɗaya daga cikin ƴan tawagar me suna Ado Salisu ya shaidawa manema labarai.

A cewar Salisu “Motar da suke ciki mallakar hukumar wasanni ta jihar Kano tana dauke da mutane 35, inda ta faɗa kasan wata gada a garin Dakatsalle, wadda yanzu haka ragowar mutanen suna asibiti ana ba su kulawar gaggawa”.

Hatsarin dai ya rutsa da yan jaridu, jami’an lafiya, ‘yan wasa da kuma wakilan hukumar wasannin ta Jihar Kano.

Gwamnan Kano da mataimakinsa, da Kwamishinan wasanni da al’ummar jihar Kano ke ta bayyana kaɗuwarsu jajentawa dangane da faruwar wannan iftila’i.

By ukarofi