Ƙungiyar ‘yan jarida a Katsina ta taya tsohon gwamnan jihar Masari murnar cika shekara 75 da haihuwa

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Ƙungiyar ‘yan jarida reshen kafofin yaɗa labarai(correspondant’s chapel) a Jihar Katsina ta bayyana Masari a matsayin Dattijo mai hangen nesa.

A takardar sanarwa ɗauke da sa hannun sakataren Ƙungiyar Zubairu Idris, ƙungiyar ta bayyana tsohon gwamnan a matsayin mutumin mai dattaku da tausayawa wajen jagorantar jihar a tsawon shekaru takwas yana riƙe da muƙamin gwamnan jihar.

“Babu shakka tsawon mulkin sa a jihar Katsina a samu canje-canje da dama musamman kan samar da ababen more rayuwa da kawo haɗin kan al’ummar jihar”inji sanarwar.

Takardar sanarwar ta ce ganin irin waɗannan baiwa da Allah ya ba Masari, shugaban ƙasa Bola Tinubu ya bashi muƙamin shugaban hukumar bada tallafin ilimi mai zurfi TETFUND

Ƙungiyar tayi masa fatan Allah ƙara masa lafiya da tsawaicin kwana da kyakkyawar farko.

Haka kuma Ƙungiyar ta yi fatan tsohon kakakin majalisar zai yi amfani da matsayin da ya ke riƙe da shi wajen bada gudunmawar cigaban jihar musamman ta fanin ilimi mai zurfi.

By ukarofi