Kai wa jami’an tsaro hari hatsari ne ga tsaro

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Kawo yanzu dai labarin kisan gillar da aka yi wa wani Babban Jami’in ɗan sanda (DPO) CSP Baba Ali Muhammed, a ƙaramar Hukumar Rano ta Jihar Kano ya gama karaɗe ƙasar nan. Rahotanni daga kafafen watsa labarai daban-daban na bayyana irin yadda lamarin ya auku, wanda har ya tunzura matasan yankin ga yin wannan aika-aika.

A wata sanarwa da Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kano ta fitar, an bayyana cewa, lamarin ya auku ne a dalilin kama wani matashi mai suna Abdullahi Musa, wanda ke sana’ar gyaran babur da misalin ƙarfe 8:15 na daren ranar 25 ga watan Mayu, 2025. An kama shi ne bisa ƙorafin da aka shigar a gaban ofishin ’yan sanda na yankin cewa yana mummunan tuƙi a cikin gari, kuma ana zargin sa da shan kayan maye. Bayan an kama shi, a cewar sanarwar, sai aka lura da yanayin sa ba a hayyacinsa yake ba, don haka aka garzaya da shi Babban Asibitin Rano, a inda ya ce ga garin ku nan, washegari da ƙarfe 6 na safiyar ranar 26 ga watan Mayu. Bayan da labarin rasuwar sa ya bazu a gari ne sai wasu ɓangarin matasa da suka fusata suka farwa ofishin ’yan sandan garin suka farfasa ginin da wasu motoci, tare da sanya wuta a wani sashin ginin, da sace wasu kayan aiki. A yayin wannan ɗanyen aikin ne aka jikkata Babban Jami’in ’Yan Sandan (DPO), wanda aka garzaya da shi asibiti domin samun kulawar likitoci, daga bisani kuma rai ya yi halin sa.

Aukuwar wannan mummunan al’amari ya haifar da zaman ɗarɗar a garin na Rano, yayin da ’yan sanda suka sanar da kama mutane 27 da ake zargi da hannu a wannan ta’asa, sannan kuma ake cigaba da gudanar da bincike.

Babu shakka wannan al’amari da ya faru bai dace ba, kuma kuskure ne a ce har wasu matasa na ganin sun fi ƙarfin hukuma, kuma babu wanda ya isa ya tsawatar musu. Don haka sun ɗauki doka a hannun su, ta hanyar ɓarnata dukiyar gwamnati, da kai wa jami’anta mummunan hari.

Wannan ba abu ne da za a lamunta ba, kuma bai kamata shugabannin al’umma a yankin su iya barci da idanun su ba, saboda shaida ce da ke nuna akwai sakacin magabata, kuma akwai ƙalubalen tsaro mai girma a yankin. In dai har za a iya yi wa babban jami’in tsaro irin wannan aika-aika to, lamari ya ƙazance!

Kodayake wannan ba shi ne karon farko da wasu ɓatagari suka aikata irin wannan ɗanyen aikin akan ’yan sanda ba, saboda zargin yin kuskure a wajen gudanar da aikinsu, ko saboda wasu baragurbin cikinsu sun yi wani abu marar dacewa. Kamar irin abin da ya faru a lokacin zanga-zangar EndSars wanda aka lalata ofisoshin ’yan sanda da dama a ƙasar nan da jefa rayuwar wasu jami’ai da iyalansu cikin haɗari.

Jaridar Premium Times ta ranar 30 ga watan Oktoba na shekarar 2020 ta rawaito cewa, Babban Sufeton ’yan sanda na wancan lokacin, Mohammed Adamu, ya sanar da cewa an kashe aƙalla jami’an ’yan sanda 22, yayin da wasu da dama suka samu munanan raunuka. Sannan an ƙona ofisoshinsu ’yan sanda 205 a sassan ƙasar nan bakiɗaya.

Wannan lamarin ya faru ne sakamakon fushi da tunzura da aka ce matasan Nijeriya sun yi, a dalilin ayyukan cin zarafin ɗan adam da wasu baragurbin ’yan sanda ke aiwatarwa. Hakan ya haifar da babban giɓi a harkar tsaro a ƙasa, kuma ya taɓa mutunci da martabar aikin ɗan sanda. Sai dai saboda ƙwarewar aiki da sanin makama ta shugabannin ’yan sanda na lokacin, lamarin bai jima ba, aka dawo da komai kan turba. Kodayake har yanzu rundunar ’yan sanda ta ƙasa na fama da ƙalubalen ƙarancin jami’ai da rashin wadatattun kayan aiki.

Sake dawowar kai hari kan ofisoshin ’yan sanda daga ’yan daba da tsagerun matasa, a wasu sassan ƙasar nan babban abin damuwa ne sosai. Domin kuwa a yayin da ake fuskantar dawowar hare-hare da ayyukan ta’addancin Boko Haram a yankin Arewa Maso Gabas, da hare-haren ’yan bindiga kan ’yan sanda a Arewa Maso Yammacin Nijeriya, da harin da tsagerun Naija Delta da na ’yan awaren Biyafira ke kai wa kan jami’an tsaro da ofisoshin ’yan sanda. A ce an bari har wasu matasa masu kunnen ƙashi su ma za su buji ƙirji su ce za su ɗauki doka a hannu su riƙa kai wa ’yan sanda mummunan farmaki irin haka, lallai akwai abin nuna damuwa.

A ranar 21 ga wannan wata na Mayu, jaridar Tribune ta rawaito cewa wasu matasa a Kwadon da ke garin Gombe, sun kai hari kan wani ofishin ’yan sanda tare da farwa Babban Jami’in ’yan sanda na yankin, CSP Adamu Alhaji Idi, wanda suka raunata har aka kwantar da shi Babban Asibitin Koyarwa na Tarayya (FTH) da ke Gombe.

Harwayau, a garin na Gombe dai a ranar 17 ga watan Afrilu, 2025 wasu tsagerun matasa sun kashe wani jami’in ’yan sanda SC Ahmed Muhammad mai shekaru 28, yayin da yake bakin aiki tare da wasu jami’ai da ke sintiri a wata anguwa da ake kira da ƙumbiya-Ƙumbiya Kwatas.

A watan Maris na shekarar 2025, wasu tsagerun matasa masu riƙe da makamai sun far wa wasu ofisoshin ‘yan sanda a Jihar Inugu, inda har suka kashe wani jami’i guda ɗaya, mai suna Emmanuel Akpa, da ke aiki a ƙarƙashin ofishin ‘yan sanda na yankin Awgu. Rahotanni sun ce, maharan sun kai hari ofishin ne da misalin ƙarfe biyun dare, inda suka fitar da waɗanda ke tsare kuma suka sace wasu muhimman makamai.

Wasu rahotannin ma na cewa ’yan sanda biyu ne aka kashe.

A shekarar da ta gabata a Jihar Bauchi an samu rahotannin da suka tabbatar da aukuwar wani mummunan kisan gilla da aka yi wa wani jami’in ’yan sanda, Ibrahim Naziru Musa, da ke tare da rundunar kwantar da tarzoma (Mopol 10), sakamakon harin da wasu matasa ’yan Sara-Suka suka kai masa, a wata anguwa da ake kira da Sarakuna, a cikin garin Bauchi. Jaridar Wikki Times ta rawaito cewa, shi ma Naziru Ibrahim ya rasa ransa a asibiti, sakamakon sassara shi da adduna da wuƙaƙe da matasan suka yi.

Lissafin haka yake ta tafiya, daga wannan jiha zuwa waccan. Lallai akwai abin nazari sosai, musamman ga hukumomin rundunar ’yan sanda. Wajibi ne a ɗauki tsauraran matakai na kare ofisoshin ’yan sanda, da ƙara musu ƙarfin kare kansu. A ƙara ba su horo kan yadda za su inganta ayyukansu da tsare rayuwarsu, da kuma kyautata alaƙar su da jama’a. Domin alamu suna nuna cewa, wasu hare-haren ana kai su ne a matsayin ramuwar gayya ko ɗaukar fansa, sakamakon wani lamari da ya faru tsakanin ’yan sanda da tsagerun matasa, ko waɗanda aka kama ana bincike a kansu.

Jaridar Daily Nigerian ta fitar da wani rahoto da ke zargin jami’in ’yan sandan da aka yi wa kisan gilla a Rano ta Jihar Kano Bala Ali Mohammed, ya taɓa azabtar da wasu mutane biyu da ake zargin sun aikata laifi a cikin watan Yuli na shekarar 2020, a lokacin yana aiki a Jihar Bauchi, waɗanda daga bisani suka rasu, sakamakon azabtarwar da aka riƙa yi musu, a cewar jaridar. Kodayake ba wancan zargin ne ya haifar da wannan kisan gilla a Jihar Kano ba, amma ana danganta abin da mutanen garin Rano ke zargin sa a kai, abu ne da kamar a ce ya saba.

Don haka, lallai yana da muhimmanci jami’an ’yan sanda da sauran jami’an tsaro su fahimci cewa yanzu fa abubuwa sun canza ba kamar a baya ba. Jama’a sun ƙara samun wayewa da sanin haƙwoƙinsu. Haɗin gwiwa da jama’ar gari shi ne yake kawo sauƙin gudanar da aikin ’yan sanda, ba tsanani ko cin zarafin wanda ake bincike a kansa ba. Akwai buƙatar sake sabunta yadda jami’an ’yan sanda ke tafiyar da ayyukansu, musamman a ƙauyuka da ƙananan hukumomi, domin tabbatar da suna kiyaye dokokin aiki da tafiya da zamani.

Sannan, lallai al’ummar gari su sani, suna da haƙƙin tsawatarwa da sanya ido kan tarbiyyar matasan su, da haɗa gwiwa da hukumar ‘yan sanda don magance matsalar rashin tsaro a yankunan su, ta hanyar ba su haɗin kai, da bayanai masu muhimmanci. Sanya ido ana kai wa jami’an tsaro hari babban hatsari ne, ba ga rayuwar su ’yan sandan ba, har ma da al’ummar yankin bakiɗaya.

By ukarofi