‘Ya’yan mawaƙi Aminu Ala huɗu sun yi saukar Al’ƙur’ani mai girma

Spread the love

Daga MUKHTAR YAKUBU 

A ranar Asabar 17/05/2025 ne aka yi taron bikin murnar mahaddatan ƙur’ani da masu sauka da haddar izu goma daidai sama da sha biyar, Makarantar Islamiyya ta Umar Ibn Kattab Unguwar Medile da ke ƙaramar Hukumar kumbotso a Jihar Kano.

Taron ya ƙayatar matuƙa gaya domin ya sami halartar manyan mutane na daga malamai da farfesoshi da sakataren ilimi na gwamnati tare da Sarkin ɗiyan Gobir ɗamburan Sarkin Gobir. Aminu Ladan Abubakar Ala.

‘Ya’yan Mawaƙi Aminu Ladan Abubakar Ala guda huɗu wato Imammu Zahbi Aminu Ladan Abubakar Ala, Aisha Humaira Aminu Ladan da Amina Aminu Ladan Abubakar Ala, da Hasina Aminu Ladan Abubakar Ala. Suna cikin ɗimbun ɗaliban da suka yi nasarar samun saukar Alkur’ani da aka yi a makarantar .

Da yake tofa albarkacin bakin sa dangane da taron saukar Alƙur’anin, Aminu Ladan Abubakar Ala ya nuna godiya ga Allah da ya kasance ɗaya daga cikin manyan baƙi da aka gayyata a wajen taron. Sannan kasancewar sa ɗaya daga cikin iyayen yaran da suka yi sauka a makarantar. Aminu Ladan Abubakar Ala ya taya ɗaliban da suka yi nasarar samun saukar Alƙur’anin, tare da yaba wa malamai da iyayen makarantar saboda ƙoƙarin su wajen bayar da kulawar su ga ɗaliban.

 Daga ƙarshe ya ce “Da fatan wannan hidima da ake yi wa Alƙur’ani Allah ya sa ya zama abin hujja a gare mu ranar neman tsira.”

By ukarofi