
Daga BELLO A. BABAJI
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ne ya jagoranci ayarin don isar da saƙon jajen Shugaba Bola Ahmad Tinubu bisa hatsarin mota da ya rutsa da ƴan tawagar jihar Kano a kan hanyar Kaduna zuwa Kano.
Lamarin ya auku ne a lokacin da ƴan wasan suke kan hanyar dawowa daga gasar wasannin motsa jiki da aka gudanar a jihar Ogun.
Mataimakin Shugaban Ƙasar ya kuma jajenta wa iyalai da al’ummomin da bala’in ambaliyar ruwan sama ya shafa a Ƙaramar Hukumar Mokwa ta jihar Neja da kuma waɗanda suka rasa rayukansu a yayin iftila’in.
