
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya ayyana ranar Litinin a matsayin lokacin hutu ga ma’aikata domin taya jimami ga iyalan ƴan wasa 22 da suka rasu a wani hatsarin mota a lokacin da suke koma wa Kano daga Jihar Ogun.
Kakakin Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa a wata takarda, ya ce gwamnati ta zaɓi ranar Litinin ne domin bai wa al’umma damar yin addu’o’i ga mamatan tare da iyalansu.
Daga cikin waɗanda suka rasu akwai ƴan wasan guje-guje da tsalle-tsalle da koca-kocai da kuma jami’an wasanni, waɗanda suke wakiltar jihar a wasanni da dama a Babban Bikin Wasanni na Ƙasa.
Ya kuma ce, a madadin gwamnatin jihar da al’ummarta, yana miƙa saƙon ta’aziyyarsu ga iyalan mamatan da fatan Allah ya jiƙan su ya kiam bada haƙurin juriya.
Ya ƙara da cewa, gwamnatin jihar ta sanar da cewa za ta bada Naira miliyan 1 ga iyalan kowane ɗaya daga cikin mutane 22’n da suka rasu, kamar yadda Mataimakin gwamnan jihar, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya bayyana.
Ya kuma ce, gwamnatin za ta samar da kayan abinci da wasu kayayyakin rage raďaďi ga iyalan mamatan.
