Gwamna Sule yana inganta harkokin aikin hajji a Nasarawa, cewar Hon. Ibrahim Nana

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

ɗan majalisa dake wakiltar mazaɓar Keffi ta Kudu a majalisar dokokin jihar Nasarawa wanda shine kuma shugaban kwamitin ayyukan al’umma da harkokin mahajjata a jihar, Honorabul Aliyu Ibrahim Nana ya yaba wa gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule dangane da ƙoƙari da ya ce gwamnatinsa ke yi don inganta harkokin hukumar jin daɗin alhazan jihar musamman a bana shekarar 2025 da ake ciki.

Honorabul Aliyu Ibrahim Nana wanda aka fi sani da Baba Ali ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu jim kaɗan kafin a wani babban taron bankwana da hukumar jin daɗin alhazan jihar ta Nasarawa ta shirya wa mahajjatan na bana daga jihar a harabar sakatariyar ta dake Lafiya fadar gwamnatin jihar kwanakin baya.

Ya ce tabbas kiran ya zama dole idan aka yi la’akari da yadda Gwamna Abdullahi Sule kawo yanzu yake ta ƙirƙiro sabbi da kuma ingantattun tsare-tsare dake cigaba da jawo cigaba da sauƙin harkokin hajji a jihar.

A cewar Honorabul Aliyu Ibrahim Nana gwamnan na cimma nasarar ne kuma ta nada shugabanni masu kwazo da hazaka da kuma tsoron Allah don kula da harkokin maniyyatan daga jihar da baida tallafi na musamman akai-akai a nan gida Nijeriya da ƙasa mai tsarkin don tabbatar maniyyatan ba su fuskanci matsala ba kafin lokaci da kuma bayan aikin ibadar da sauransu ta kula yarjejeniya na musamman da hukumomin Saudiya da suka dace da babban bankin Nijeriya da hukumomin kiwon lafiya da kuma uwa uba ɗaukan nauyin galibin maniyyatan da gwamnatinsa ke yi a duk shekara tunda ya hau kujerar gwamnan jihar kimanin shekaru 6 da suka wuce.

ɗan majalisar dokokin ta jihar Nasarawa Honorabul Aliyu Ibrahim Nana ya kuma yi amfani da damar inda ya taya mahajatan muryar samun damar tafiya aikin ibadar inda ya kuma shawarce su su kasance jakadun jihar nagari ta bin duka dokokin ƙasa mai tsarkin kana suyi wa jihar da ƙasa baki ɗaya addu’a don samun jinƙan Ubangiji.

Ya ƙara da cewa a matsayin sa na mamban majalisar kuma shugaban kwamitin ayyukan al’umma da harkokin maniyyatan zai cigaba da haɗa kai da gwamnatin Injiniya Abdullahi Sure ta bada nasa gagaruman gudumawa musamman a fannin kokirkiro tareda shigar da ingantattun ƙudurori cikin doka a zauten majalisar da za su cigaba da inganta harkokin jin daɗinsu a koyaushe kana ya buƙaci al’ummar jihar bakiɗaya su cigaba da ba shi cikakken goyon baya.

Wakilinmu ya binciko cewar a halin yanzu dai duka mahajjatan bana daga jihar ta Nasarawa duk suna can ƙasa mai tsarkin suna gudanar da aikin Ibadar na bana bayan an tantance su daga hukumar jin daɗin alhazan dake Lafiya Babbar birnin jihar.

By ukarofi