Tinubu ya taya Musulmi murnar sallah da kira a riƙa taimakon juna da jinƙai

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya al’ummar Musulmi a Nijeriya da duniya baki ɗaya murnar zagayowar bikin babbar Sallah, tare da jaddada muhimmancin sadaukarwa, biyayya ga Allah da kuma ɗorewar juriya a lokacin ƙalubale.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, shugaban ƙasar ya ce kwanaki goma na farkon watan Zul Hijja na cikin ranaku masu albarka, waɗanda ke cike da alkairai da kuma zaburarwa zuwa yawaita ibada.

Ya bayyana cewa, duk da ana gudanar da bikin Idin Sallah Babba, amma haƙiƙar tasirin ranar na koyar da mu sadaukarwa, biyayya da ƙaunar juna.

“Domin girmama wannan rana, wajibi ne mu rayu da waɗannan dabi’u kamar yadda Annabi Ibrahim (AS) ya kasance mai cikakken biyayya ga umarnin Allah, kuma kamar yadda Manzonmu Muhammadu (SAW) ya koyar da mu,” inji shi.

Shugaban ya yi kira ga al’ummar Nijeriya da su ƙara dagewa da juriya, da nuna goyon baya ga cigaban ƙasa, yana mai tabbatar da cewa gyare-gyaren da gwamnatinsa ke aiwatarwa na samun nasara kuma suna daɗa kawo sauyi.

“Mun fuskanci ƙalubale, amma mun wuce lokaci mafi wahala. Mun shigo sabon zamani na sabunta fata da wadata,” in ji shi.

“Mun fara ganin canji ta fuskar tattalin arziki kuma nan ba da jimawa ba, al’umma za su fara jin daɗin sauyin.”

Shugaban ƙasar ya kuma bayyana cewa, manufar gyare-gyaren da ake aiwatarwa ba wai don samun gyaran a rubuce ba ne kaɗai, sai dai don inganta rayuwar ‘yan ƙasa da gina tushe mai ɗorewa ga tattalin arzikin ƙasa. Ya ce gwamnatin sa za ta ci gaba da aiki a bisa muradun al’umma don tabbatar da jin daɗin kowa.

A yayin da ake shagulgulan Sallah, Shugaba Tinubu ya buƙaci Musulmai da su nuna ƙauna, tausayi da taimakon juna musamman ga marasa galihu. Ya kuma yi addu’ar Allah ya karɓi ibadu da sadaukarwar da aka gudanar a wannan rana.

Ya kuma bayyana baƙin cikinsa kan ambaliyar da ta faru a Mokwa, Jihar Neja, a ranar 28 ga Mayu, wacce ta haifar da asarar rayuka da dukiyoyi. Ya yi kira ga al’umma da su taimaka wa gwamnati wajen tallafa wa waɗanda abin ya shafa.

A ƙarshe, ya bukaci a ci gaba da yin addu’a ga jami’an tsaro da ke fuskantar haɗari don kare rayuka da dukiyoyin al’umma, da shugabanni a dukkan matakai, da kuma samun zaman lafiya a Nijeriya da duniya baki ɗaya.

By Babaji