Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamna Dikko Raɗɗa na Jihar Katsina ya roƙi Musulmi da ke arfa da waɗanda ke yin azumi a gida su sanya Jihar Katsina addu’ar zaman lafiya da ƙarshen matsalar tsaro.
Gwamna yayi wannan roƙon ne a saƙon taya al’ummar jihar zagayowar sallah babba.
Gwamnan wanda na ɗaya daga cikin miliyoyin musulmin duniya da ke gudanar da aikin Hajj a ƙasar Saudiyya,ya kuma yi kira ga Musulmin jihar da su tuna da mabuƙata yayin buƙatuwan sallah.
Ya nemi haɗin kai da goyon baya na al’ummar jihar don kawo cigaban jihar.
Gwamna Dikko Raɗɗa yayi waiwayi kan shekara biyu da yayi akan mulki inda ya bayyana cewa an sami cigaba ta fanni da dama a jihar.
Ya ce harka noma , kiwon lafiya, harkokin noma da sauran ababen more rayuwa na daga cikin ayyukan da gwamnatin sa ta sami nasara a kai.
Gwamnan ya miƙa godiyar sa ga jami’an Sojoji, ‘yan sanda da jami’an tsaro na al’umma da sauran jami’an tsaro da ke yaƙi da ta’addanci a jihar.
Sai yayi kira ga al’ummar jihar da su cigaba da ba jami’an tsaron goyon baya da yi masu addu’ar kariya da samun nasarar dawo da zaman lafiya a jihar.
