A yau Juma’a ne ake gudanar da Sallar Layya wadda aka fi kira da Babbar Sallah, bayan gudanar da hawan Arfa a ranar Alhamis.
Tuni dai Gwamnatin Tarayya Nijeriya ta ayyana ranakun Juma’a da Litinin a matsayin ranakun hutu ga ma’aikatan ƙasar domin bikin Babbar Sallah.
Ranakun za su dace da 6 da kuma 9 ga watan Yuni da muke ciki.
Ministan harkokin cikin gida Olubunmi Tunji-Ojo ne ya sanar da hutun a madadin gwamnatin tarayya, yana mai taya al’ummar Musulmi murnar zagayowar bikin.
Ministan ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa gyare-gyare da tsare-tsare da suka shafi jama’a da aka yi, a ci gaban ajandar sabunta ƙasa na gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, shi ne dawo da Nijeriya kan turbar ci gaba.
Yayin da yake yiwa al’ummar Musulmi barka da Sallah, Ministan ya buƙaci dukkan ‘yan Nijeriya da su haɗa kai da gwamnati mai ci a ƙoƙarinta na dawo da martabar Nijeriya a matsayin ƙasa mai girma.
A lokacin wannan sallar ne ake yin layya wato yanka dabba don sadaukarwa ga Allah SWT. An fara layya a lokacin annabi Ibrahim (AS). Daga nan aka ci gaba da yinta a duk ranar 10 ga watan Dhul Hajj a kowace shekara.
Yin Layya wata hanya ce ta bin umarni da yin biyayya ga mahalicci. Don haka ɗa’a ga Allah da iyaye da kuma shugabannin al’umma ita ce ingantacciyar hanyar sadaukarwa. A fahimta sadaukarwa ba ta tsaya kaɗai ga bin umarnin yin layya ba ne, a’a, ta ƙunshi yin biyayya ga umarnin Allah SWT da duk wata sadaukarwa don ci gaban jama’a. Samar da ingantaccen shugabanci da zai amfani jama’a da ƙasa na ɗaya daga cikin ingantacciyar sadaukarwa.
Kamar yadda shari’a ta tanadar ana so duk wanda ya samu ikon yin layya sai ya yi sadaka ga makwafta da kuma sauran al’umma musamman ma marasa ƙarfi. A lokacin sallar layya ana so a riƙa ziyartar juna hakan zai ƙara danƙon zumunci ya kuma samar da haɗin kai, ya kuma sanya a yafe wa juna laifuffuka da aka aikata.
Shugabanci da ke cike da tawali’u da kamala da gaskiya da adalci da kuma rungumar jama’a wasu halaye ne da ke tabbatar da ingantacciyar sadaukarwa. Waɗannan halaye a yanzu sun yi ƙaranci a tsakanin shugabanni da kuma talakawan ƙasar nan. Don haka ya kamata zaɓaɓɓun shugabanni da waɗanda aka naɗa da na wucin gadi da na addini su riƙa amfani da waɗannan halayen don dawo da ƙasar nan turba daidai don a samu ci gaban tattalin arziki da bunƙasar ƙasar nan.
Muna fata gwamnati za ta yi amfani da wannan lokacin don ɗaukar ƙwararan matakai da za su magance talauci da cin hanci da rashawa da kuma rashin aikin yi da suka hana ƙasar nan sakat. Yin hakan zai rage raɗaɗin talaucin da ’yan Nijeriya suka samu kansu a ciki.
Ya kamata kowane shugaba ya riƙa sanya al’ummarsa a zuciya, ya riƙa yi musu abubuwan da za su inganta rayuwarsu.
’Yan siyasa su daina ɓatar da matasa ta hanyar raba kawunansu don biyan buaatar ƙashin kansu.
Munanan abubuwa sun faru a Nijeriya a shekarun da suka gabata musamman ma matsalar tsaro da ta hana ƙasar nan motsawa nan da can, don haka gwamnati ta tashi tsaye wurin magance matsalar da ke neman kai ƙasar nan ƙas. Ta yi amfani da hanyoyin hikima ba na nuna ƙarfi ba ciki har da tattaunawa wurin kawo ƙarshen matsalar tsaro. Haka duk wata ƙungiya ko mutum da ke da wani ƙorafi to ya bayyana shi ta hanyar hikima ba amfani da makamai ba.
Tayar da ƙayar baya ko tayar da zaune tsaye ba su ne sahihan hanyoyin bayyana rashin adalci ko take haƙƙi ba. Hakan sai dai ya ƙara ta’azzara al’amarin ba wai samar da baƙin zaren matsalar ba.
Duk wazansu hanyoyin da za su samar da zaman lafiya su ake so, a kuma yi amfani da saƙonnin da za su kawo zaman lafiya a kowane yanki.
Ya kamata Musulmi su yi amfani da darussan sallar layya wajen kawo zaman lafiya a ƙasar nan, su kuma yi amfani da waɗannan darussan wurin yi wa shugabanni addu’a don su samar da kyakkyawan shugabanci.
A ƙarshe, Jaridar Blueprint Manhaja tana fata Allah Ya maimaita mana cikin ƙoshin lafiya da wadata da kuma kwanciyar hankali. Barka da Sallah!
