Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Fitaccen marubucin adabi a Nijeriya, Wole Soyinka, ya yaba wa tsohon gwamnan jihar Ribas, Chibuike Amaechi kan ƙin amincewa da Bola Tinubu a lokacin zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC a shekarar 2022.
Soyinka ya bayyana haka ne a Abuja ranar Asabar a wajen bikin cikar Amaechi shekaru 60 a duniya, wanda ya yi gwamnan jihar Ribas daga 2007 zuwa 2015.
Mawallafin litittafan wasan kwaikwayon ya ce, ya ji daɗin bijirewar da Amaechi ya yi a zaɓen fidda gwani, wanda ya bayyana kai tsaye daga Abu Dhabi.
“Babban dalilin da ya sa na zo nan a yau – na farko shi ne na yaba da jajaircewar Rotimi Amaechi,” inji shi.
Soyinka ya ce, Amaechi ya yanke shawarar ci gaba da tsayawa takara kamar yadda Tinubu ya bijirewa gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo.
Idan dai za a iya tunawa, Tsohon ministan sufuri na Nijeriya, Rotimi Amaechi ya ce tun farkon fara gangamin yaain neman zaɓen 2023 ne ya yanke shawarar ba zai zaɓi Shugaba Bola Tinubu ba, inda ya ce sun haɗu gaba da gaba, kuma ya faɗa a take cewa shi ba zai zaɓe shi ba.
Amaechi ya ce hakan ya sa ya cika alƙawarin da ya ɗaukar wa kansa na ƙin taimakon yaƙin zaɓen Tinubu, saboda a cewarsa ya gano tun da wuri cewa aikin zai yi wa shugaban nauyi na mulkin Nijeriya.
Amaechi ya bayyana haka ne a wajen taron murnar cikarsa shekara 60 a duniya wanda aka yi a Abuja.
“A Yola muka haɗu da Tinubu, inda na faɗa masa cewa ni ba zan goya masa baya ba. Kuma ban yi ba, kuma ban zaɓe shi ba. Magana ce ta tunanin ba zai iya ba.
“Wasu daga cikinmu da suke nan ma sun yi zaɓen ne saboda addini da ƙabilanci. Kawai ana wasa da hankalin mutane ne su yi zaɓe bisa la’akari da addini ko ƙabilanci. Kuma ga inda hakan ya kawo mu nan.”
Da yake magana game da haɗakar siyasa, Amaechi, “za mu haɗu da jam’iyyun adawa ne idan su ne za su fitar da mu daga cikin ƙangin da muke.”
