
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Alhamis a matsayin lokacin hutu domin bikin zagayowar Ranar Demokraɗiyya na shekarar 2025.
Babbar Sakatariyar Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida, Magdalene Ajani ba bayyana hakan a wata takarda, ranar Lahadi.
Ta ce, Ministan Ma’aikatar, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo ya sanar da hakan a madadin Gwamnatin, inda ya taya al’ummar Nijeriya murnar cika 26 na mulkin farar hula ba tare da samun tsaiko ba.
Ya bayyana cewa, zaɓen June 12 da aka soke a ƙasar yana wakiltar tafiyar da aka ɗauko na gina ƙasa mai cike da gaskiya da adalci da wanzuwar zaman lafiya gami da tabbatar da samun gobe mai kyau a Nijeriya.
Ya kuma jaddada aniyar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na cigaba da ƙoƙarin samar da gobe mai kyau (renewed hope) ga ƙasar duba da irirn tsare-tsaren da ya ke shimfiɗawa.
