MOPPAN ta jajenta wa Adam A. Zango kan hatsarin da ya yi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Ƙungiyar masu shirya fina-finai ta Ƙasa (MOPPAN) ta jajenta wa jarumi Adam A. Zango game da iftila’in da ya same shi na hatsarin mota.

A sanarwar da Sakatarenta, Dakta Ibrahim Gumel ya fitar, MOPPAN ta yi addu’ar fatan Allah ya ba shi lafiya tare da kiyaye sake aukuwar irin haka a nan gaba, da kuma fatan hakan ya zamo kaffara a gare shi.

Haka kuma, ya ce a madadin abokanansa na arziƙi da na sana’a tare da masoya suna masa jaje da fatan samun sauƙi cikin ƙanƙanin lokaci.

Dakta Gumel ya yi addu’ar samun nasara ga masana’antar Kannywood tare da kare ta daga dukkan sharri.

By Babaji