Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Adulrahman Bello, babban wanda ake zargi da kashe wata ɗalibar makarantar sakandare ta jihar Kwara, Hafsoh Lawal, ya shaida wa kotu a ranar Larabar da ta gabata cewa shi kaɗai ya aiwatar da yanka marigayiyar bayan ya sha barasa.
Da yake ba da shaida a gaban mai shari’a Hannah Ajayi ta babbar kotun jihar, yayin da yake buɗe kariyarsa, wanda ake zargin ya ce waɗanda ake tuhumar ba su da hannu a lamarin.
Abdulrahman Bello ya kuma shaida wa kotun cewa ya yi amfani da wuƙa wajen yankata da jami’an ‘yan sanda suka gano a gidansa mai ɗaki biyu da ke unguwar Olunlade a Ilorin, babban birnin jihar, wajen farɗe gawar marigayiyar.
Wanda ake zargin, wanda ya musanta cewa ya kashe marigayiyar, ya ce Hafsoh ta rasu ne a lokacin da ta yi haƙi a lokacin jima’i sakamakon kamuwa da cutar asma.
“Na fita ne domin in samo mata inhaler, sai na lura tana haki saboda tana da asma, a lokacin da na dawo ɗakin ta rasu, don haka na bar wurina na ɗauki barasa na dawo na yanka sassan jikin gunduwa-gunduwa,” ya shaida wa kotu.
A lokacin da daraktan masu shigar da ƙara na ƙasa (DPP) suka yi masa tambayoyi, babban wanda ake zargin ya kuma tabbatar wa kotun cewa bai kira wani makwabcinsa da lamarin ba, kuma bai kai rahoto ofishin ‘yan sanda ba ko kuma kai gawar marigayiyar asibiti, “saboda ina tsoron mahaifinta.”
DPP ta bayyana wanda ake zargin cewa zubar jini da sassan jikin marigayiyar da aka samu a wurinsa ba su ruɓe ba bayan kwana biyar da faruwar lamarin, saboda an nutsar da su cikin barasa don adanawa.
Sai dai wanda ake zargin, ya musanta cewa ya ajiye jini da hannu, da gangan don yin tsafin neman kuɗi.
Ya ce ya yi nadamar duk wani mataki da ya ɗauka a kan lamarin, inda ya ce ya yi matuƙar baƙin ciki.
Babban wanda ake zargin, wanda ya dage da cewa shi bai kashe marigayiyar ba, ya ce yana sonta, “saboda ba zan iya haɗuwa da irinta ba, ta kula da rayuwata, har ma na shaida wa ‘yan sanda cewa ta sa na yi jarrabawar NABTEB ta 2024. Kuma ta sa na ɗauki fom ɗin JAMB a shirye-shiryen jarrabawar da aka kammala. Ta yi fice a rayuwata.
Ya ce ‘yan sanda sun azabtar da shi ya ce a cikin hoton bidiyon da aka gabatar a gaban kotu, ya ce ya sanya guba a abincin da marigayiyar ta ɗauka kuma ya shake ta ya kashe ta.
Dukkan wadɗnda ake tuhumar su huɗu a kan lamarin sun musanta labarin kisan marigayiyar a lokacin da suke ba da shaida a gaban kotu.
A halin da ake ciki, dukkanin lauyoyin da ke kare waɗanda ake ƙara, ba tare da amincewa ba, sun ba da shawarar kwanaki bakwai don gabatar da adiresoshinsu a rubuce, a lokaci guda, a gaban kotu, yayin da lauyan masu gabatar da ƙara ya buƙaci a ba su kwanaki 10 don gabatar da nasa, bayan da lauyoyin masu karesu sun yi aikinsu.
Mai shari’a Hannah Ajayi, wadda ta amince da buƙatun, daga baya ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 2 ga watan Yuli, 2025, domin karɓar adireshin na ƙarshe.
