
Daga BELLO A. BABAJI
Baya ga harin Isra’ila akan ma’ajiyar makaman nukiliyar Iran, wanda ya yi sanadin mutuwar manyan sojoji da masana kimiyya da hallaka mutane da dama.
Jakadan Iran ya shaida wa majalisar tsaro ta Majalisar Ɗinkin Duniya cewa fararen hula sun fi yawa daga cikin waɗanda aka kashe.
Ya bayyana hakan ne jim-kaďan bayan Iran ta mayar da martani da makamai masu linzami a babban birnin kasuwancin Isra’ila, wato Tel Aviv, wanda ya raunata aƙalla mutane 34.
Isra’ila ta tsokano faɗan ne duba da yadda ƙarfin makaman nukiliyar Iran a Tehran ya ke cigaba da bunƙasa.
A tsawon shekaru, Isra’ila tana barazanar kai wa Iran hari, wanda hukumomin Amurka suka yi ta ƙoƙarin dakatarwa duba da yadda hakan ka iya haddasa babban yaƙi a yankin Gabas ta Tsakiya.
Harin Isra’ilar dai ya sanya Jagoran Addini a Iran, Ayatollah Ali Khamenei cin alwashin sai ta ɗanɗana kuɗarta bisa laifin da ta aikata.
